Ina Za Mu A Nes Lebul? (3)
Ba za a iya gane haka ba har sai an fahimci yadda aka shirya da tsara wannan aukuwa daga lokacin da aka fara fafutukar samar da ’yancin kai a Najeriya, inda daga nan ne aka gina tashin-tashinar, wadda ba wai ta tsaya ga amfani da karfin tuwo da ba hammata-iska a tsakanin mabambanta ra’ayoyi ne […]
Ba za a iya gane haka ba har sai an fahimci yadda aka shirya da tsara wannan aukuwa daga lokacin da aka fara fafutukar samar da ’yancin kai a Najeriya, inda daga nan ne aka gina tashin-tashinar, wadda ba wai ta tsaya ga amfani da karfin tuwo da ba hammata-iska a tsakanin mabambanta ra’ayoyi ne ba kurum, ko kuma tayar da kayar baya da ihuce-ihuce a fagen siyasa da kashe-kashe, babu gaira, ba dalili, inda ta zame kandagarki wajen ciyar da ’yan Adam gaba kadai ba.
An dai ga irin haka da dama a mabambantan lokutta, musamman a lokacin da ’yan mulkin mallaka da Sarakuna ke kan gadon mulki, tare. A daidai wannan lokaci ne aka take hakkin ’yan adawa ko talakawa, aka shiga muzguna wa duk wani da a ba a tare da shi, aka hana yawancin mutane damar zama ’yan kasa, cikakku, musamman inda aka hana wasu yin amfani da damar su ta zaben wanda suke so, ko a matsa musu su zabi wani can daban ko a hana su yin kamfen (yakin neman kuri’a), ko rashin daidaito wajen yin zabe da rashin ’yancin jefa kuri’a da yarda ko rashin yarda da sakamakon zabe bisa amincewa da abin da jama’a suka zaba, uwa-uba hana maigida samun hanyoyin ciyar da iyalinsa ko a sa masa wasu matakai da za su hana shi ci gaba ta kowace irin hanya, yana tare da hukuma ne ko kuma dan adawa ne. Ta haka aka shigo da tsarin da ke tauye wasu, ya daga wasu.
A wancan lokacin, yawancin ’yan adawa sun fuskanci matsi da tashin hankali saboda sun yi wadansu abubuwa da hukuma ke ganin ba “daidai” ba ne, kamar sanya tutar jam’iyya a keke ko sa bajen jam’iyya a gaban aljihun riga ko kuma kin da wasu ke yi na zuwa gandun Sarki domin noma ko zuwa hakar kuza a kwazazzaban Filato, ko noma hatsin kudi maimakon na ci. ’Yan mulkin mallaka sun taimaka wa Sarakuna da Shugabanin En’e wajen dankwafar da ’yan adawa da masu neman hakki, an kuma yi haka ne ba tare da boye zaluncin ba. An dai ga yadda aka shiga kwacen kayan ’yan adawa; irin su gonaki da dabbobi da keken shanu ko kuma kwana da amaren ’yan adawa, a lokacin mazada da dai sauran su. Ire-iren wadannan tashin-tashina suna da yawan gaske, sun kuma hada da kisan gillar ’yan adawa da hukumomin En’e-En’e suka asassa, tattare da taimakon ’yan doka da alkalai ta amfani da daurin gindin jam’iyyar NPC, tattare da taimakon Turawan mulkin mallaka a gefe guda.
Babar manufar Turawan mulkin mallaka ita ce su yi amfani da jami’an En’e da Sarakuna domin su tabbata an kawar da duk wadansu alamun bore da turjiya a tsakanin al’ummar Arewa, sai dai ba su samo nasara ba, yaki da bijire wa ayyukan zalunci da danniya da aka san jama’ar Arewa da su ba su kau nan take ba, wanda shi ya jawo jan daga a wadansu Larduna na Arewa. Haka ya faru ne domin shekara 100 da Daular Usumaniya ta yi a daron kasa ta taimaka wajen gina jama’a masu tsoron Allah da kyamar zalunci da cin amana da rashawa, don haka akwai gyauron ire-iren wadannan jama’a ko da Turawa suka kunno kai, suka amshe mulkin Arewa, shigowar su ma ya samar da wani sabon faifai ne na hada-hadar fada da ya yi da siyasar mulkin mallakar danniya da babakere.
Da yake tsarin En’e ya amince da Sarakuna, ya kuma amince da gado a matsayin hanyar hawa sarauta, ba zabe ba, sai wadansu sabbin matsaloli suka sake kunno kai daga shekarun 1930, lokacin da jama’ar yankin suka kara wayewa sosai, saboda yakin duniya da wasu suka halarta daga Arewa da shigowar ilimin zamani da kuma yawan tafiye-tafiye da wasu suka yi, suka samu bude idanunsu game da hakkin dan Adam a harkokin siyasa. Dayani da aka san da shi a matsayin tsarin falsafar Arewa, tuni ya rushe, nan take a kan soma samar da kungiyoyi ko kuma ra’ayoyi da za a iya kasa su zuwa gida biyu, akwai masu “ra’ayin rikau”, wato wadanda ke goya wa En’e baya, wannan gungu ya hada da sarakuna da tajirai da malamai, burinsu shi ne su ga an kwato mulki daga hannun ’yan mallaka (Turawa), zuwa ga ’yan mallaka (na gida), karkashin kulawar Sarakuna, a lokacin da aka samu ’yancin kai, ba tare da wani canji ba, su kuma Turawan mulkin suka goya musu baya ta fuskoki daban-daban. Kungiya ta biyu ko kuma a ce masu ra’ayi daban da wannan su ne ake kira da ’yan “neman canji”, wadanda su kuma burinsu a kawo sauyi ko ta wace irin hanya, musamman daga abin da aka saba gani na zalunci a Arewa zuwa wani sabo, kuma mai ma’ana. Ga irin wannan kungiya ko masu irin wannan ra’ayi, hukumar En’e da kuma Sarakuna, masu mulki tare da Turawa “sun butulce wa musulunci ne,” wannan ya sanya masu wannan ra’ayi suka shiga babatu game da mulkin danniya da zalunci da Sarakuna ke yi tare da taimakon hakimai da dagatai da kotunan alkali da ‘yan doka. Haka abin ya dinga gudana har zuwa lokacin da aka samar da kungiyoyi da jam’iyyun siyasa.
Ko kafin hakan ta samu ana da manunai da ke alamta cewa lallai za a sami shan daga tsakanin tagwaitattun jama’ar arewa, hakan ya jawo ra’ayoyi suka yawaita da samar da littattafai da suka zama abubuwan dogora wajen canza da kyautata tunanin jama’a tun kafin zaman tare ya watse. Misali, a shekarar 1944 aka samar da kungiyar siyasa ta farko, wato Kungiyar ci Gaban Arewacin Nijeriya, a cikin wannan kungiya akwai jama’a mabambanta ra’ayoyi, kamar su Abubakar Imam, Wazirin Zazzau, Malam Julde, Malam Jumare, R.A.B. Dikko, John Garba da Sarkin Zazzau Jafaru da Razdan da Di’o da wasu gaggan jama’a da dama da ke zaune a Zariya. Wannan kungiya ba ta dade ba ta wargaje, saboda dalilai masu dama. Na daya, zaman tare don tattauna batutuwa, inda ake dauke da Sarki da majalisarsa da Razdan da Di’o da wadansu ma’aikatan gwamnati bai yi wa gwamnati dadi ba, kingin kiris da wasu sun rasa mukamansu. Na biyu, tunani da ra’ayoyin wadansu daga cikin ‘yan kungiyar ya saba ko kuma ya yi wa saura fintinkau, daga ciki akwai irin su Sa’adu Zungur wanda ke ganin cewa abubuwa ba su tafiya yadda ya kamata a Arewa ta fuskoki da dama, musamman danne wa mata hakki, a harkar neman ilmi. Saboda wannan ra’ayi nasa ne ya dinga kira a irin wannan taro da a sakar wa mata mara su nemi ilmi kamar maza. Ya yi wannan kira ta amfani da ayoyin Kur’ani da Hadisai. Irin wannan “tsageranci” da wasu irin sa daga su Sa’adu Zungur da masu ra’ayinsa suka jawo Turawan mulkin mallaka da jami’an En’e suka rushe kungiyar, aka tarwatsa masu tada-zaune-tsaye, irin su Sa’adu Zungur, aka tura shi Anchau wai ya je ya yi yaki da kudan tsando, in da a can ne ya kwaso cutar da ake jin ta yi ajalinsa yana da matsakaitan shekaru.
Za Mu Ci Gaba