Ina za mu a Nes Lebul? (4)

Abin da ya faru a Zariya da soke rajistar Kungiyar Ci gaban Arewacin Najeriya bai hana an ci gaba da yaki da danniya ba, musamman bayan kammala Yakin Duniya na Biyu (wato yakin Hitla), barbazuwa da watsuwa da yin bore da turjiya karuwa suka yi a wasu sassan kasashen Hausa. An ga haka a Lardin […]

Ina za mu a Nes Lebul? (4)
Ina za mu a Nes Lebul? (4)

Abin da ya faru a Zariya da soke rajistar Kungiyar Ci gaban Arewacin Najeriya bai hana an ci gaba da yaki da danniya ba, musamman bayan kammala Yakin Duniya na Biyu (wato yakin Hitla), barbazuwa da watsuwa da yin bore da turjiya karuwa suka yi a wasu sassan kasashen Hausa. An ga haka a Lardin Bauchi (inda Sa’adu Zungur ya koma da zama a 1946) saboda rashin lafiya, zuwa Lardin Sakkwato da Katsina, inda aka shiga tattauna batutuwa na jawo hankalin talakawa zuwa ga matsalolin Arewa, musamman abubuwa da suka shafi kyamar da ’yan Arewa suka nuna game da halartar yakin Hitla, ko zuwa hakar kuza a kwazazzaban kasar Filato da kuma koke-koke kan yadda Turawa ke kwashe hatsin da ake nomawa a Arewa, ana kai wa sojoji da ke fagen yaki, maimakon a ciyar da talakawa.

Yawancin ire-iren wadannan koke-koke gwamnatin mulkin mallaka da hukumomin En’e da sarakuna ba su yi saurin hana aukuwarsu ba, sai ma suka kara taimaka musu bisa tunanin cewa in suka hau musu kawara za a iya yin bore da tashin hankali. Razdan-Razdan na larduna da wasu sarakuna da dama sun taimaka musu ta hanyoyi daban-daban, musamman ta ba su shawara su kafa kungiyoyin gama-kai da taimakon juna, ta haka za a iya saurarensu, a kuma dubi kokensu. Wannan dama ce wadansu daga masanan Arewa suka yi amfani da ita, suka samar da kungiyoyin siyasa a kaikaice. A can Bauchi an samar da Kungiyar Ci gaba da Raya Bauchi, a Zariya an samar da Kungiyar Zumunta, a Sakkwato kuwa aka samar da Kungiyar Walwala ta Matasan Sakkwato, a Kano kuma Kungiyar ’Yan Kasa ta Lardin Kano da sauransu.

Kamar yadda aka gani hada-hadar siyasa irin ta jam’iyya ba ta kankama ba sai daga karshen shekarun 1940, kuma su wadannan jam’iyyun siyasa sun samo asali ne daga iren-iren wadancan kungiyoyin gama-kai da aka ambata a baya. Ita dai Jam’iyyar Mutanen Arewa (NPC) har zuwa 1951 ta kunshi hadakar kungiyoyin da suka hada da Jam’iyyar Mutanen Arewa da Jam’iyyar Jama’ar Arewa da Kungiyar Ci gaba da Raya Bauchi da Kungiyar Zumunta ta Sakkwato da kuma Kungiyar ’Yan Kasa ta Kano.

A farkon kafuwarta, Jam’iyyar NPC ba ta da wata manufa daban da sauran jam’iyyun siyasar zamanin, wato yaki da jahilci da lalaci da zalunci, haka kuma da rusa Majalisar Sarakuna ta arewa, da ba mata dama su shiga majalisa da kuma yin zabe da yin gyaran fuska ga hukumomin En’e ta dace da zamani. Wannan ne ya sa da farko ake jin cewa Jam’iyyar NPC ta kasance jam’iyyar neman sauyi da neman ci gaba, wadda ita ma ta kasance mai bacin shugabancin sarakuna da ’yan mulkin mallaka, wannan ne ya sa da farko aka hana jami’an gwamnati shiga cikin jam’iyyar.

Ita kuma Jam’iyyar NEPU ta samo asali ne daga kungiyoyi biyu masu kama da juna. Kungiya ta farko ita ce gyauron ’yan neman canjin da suka baro NPC bayan kaddamar da jam’iyyar a 1951, sai kuma uwar kungiyar ta asali wato NEPA, wadda aka kafa tun a 1946 da niyyar hada kan jama’ar Arewa. Dangane da haka ne za a iya cewa NEPU tun azal ba ta da wani haufi na inda ta sa gaba, ba ta kaunar tsarin mulkin mallaka da kuma sarakunan da suka daure musu gindi.

Jam’iyyar NEPU ta sha bamban da Jam’iyyar NPC ta kowace irin fuska, burinta shi ne ciyar da tattalin arzikin kasa gaba da kuma fitar da talaka daga kangin bauta, musamman na Turawan mulkin mallaka da sarakuna. Bambancin wadannan jam’iyyau biyu ya kara fitowa fili daga shekarar 1951, ta fuskar wadanda suka kasance magoya bayansu da irin dangantakar jam’iyyun da sarakuna ko masu mulki na En’e ko ’yan mulkin mallaka. Ita dai NPC tuni ta watsar da shigar bunun da ta yi na neman zama jam’iyyar canji ta koma jam’iyyar danniya, wadanda suka cika ta ba su wuce ma’aikatan gwamnati da hakimai da dagattai da manyan fadawa da ke jibge a fadojin sarakuna ba, shi ya sa a Lardin Sakkwato da Adamawa yawancin ma’aikatan En’e su ne magoya bayan NPC baki daya, wata sa’a ma ba a bambantawa a tsakanin shugabannin En’e da majalisun sarakuna, a bangare guda da kuma shugabannin NPC a daya bangaren, duk jama’a guda ne!

A nata bangaren Jam’iyyar NEPU, jam’iyya ce ta ‘talakawa,’ shugabanninta da magoya bayanta ba su wuce malaman makaranta ba, sai manoma da ’yan garuwa da musunta da majema da madinka da masu faskare. Wannan yana daga cikin dalilan da suka sa NEPU to zama jam’iyyar adawa, ta shiga Allah- wadai da danniya da tsarin mulkin mallaka na Turawa da mulukiyya na sarakuna, wannan shi ya jawo rashin jituwa a tsakanin NEPU da hukuma da sarakuna. A daidai wannan lokaci ne NEPU ta fara zawarcin jam’iyyun Kudu don ta samu daurin gindin da za ta sha daga da abokan adawarta.

Wannan sabon tsari na NEPU ya sa gwamnatin mulkin mallaka ta fara tunanin yadda za ta yi da ’yan NEPU, domin tana ganin cewa batun da NEPU ke yi ta hada kai tsakanin jama’a masu ra’ayi iri daya a Arewa da Kudu zai iya tada zaune-tsaye. Saboda haka sai gwamnatin danniya ta mulkin mallaka ta shiga shiryawa da tsara hanyoyin da za su sanya NPC ce za ta gaje ta ba NEPU ba, a lokacin da aka mika mulki ga ’yan kasa bayan samun ’yancin kai. Bisa wannan tafarki ne gwamnatin mulkin mallaka ta taimaka wajen murguda sakamakon zabe, ta rika ba NPC rahotannin musamman kan yadda za a ci dunun NEPU, aka kuma shiga ba ’yan doka da alkalai damar da za su kame, su daure ’ya’yan NEPU, ba mai cewa ahir! Suka rika nuna wa NPC dakokin da za su yi amfani da su su tamke ’yan NEPU ba tare da wani ka-ce-na-ce ba.

Abin da gwamnatin mulkin mallaka ta yi bai wuce taimakawa ba domin a dakile adawa ba tare da jin tsoro ko neman boye manufa ba Daga 1954 abubuwa suka fara bayyana sosai, inda aka bayyana a fili irin yadda hukuma ta dauki wadannan ’yan adawa. Da farko dai an yi kira ga En’e-En’e su sani cewa ire-iren wadannan ’yan adawa da aka yi wa lakabi da ‘cinnaku.’ yawancin su ‘suna da tabon taba karya doka,’ ba kuma yadda za a yi a maganinsu in ba an yi musu feshin sheltos ba, hakan kuma ba zai samu ba sai ‘an karya doka da taushe hakkinsu.’