‘Ina zuwa Legas domin sayen jarirai’

A yanzu haka sashen binciken manyan laifuka na rundunar ’yan sandan jihar Legas da ke Unguwar Yaba ya tsananta bincike domin kwato dukkanin yaran da  Misis Grace Onye ta saya a jihar.Misis Grace ’yar asalin garin Onitsha ce, mai kimanin shekaru 52, ta shaida wa ’yan sanda cewa ta kware wajen haramtaccen kasuwancin saye da […]

‘Ina zuwa Legas domin sayen jarirai’

Misis Grace Onye daga dama da abokiyar huldarta NgoziA yanzu haka sashen binciken manyan laifuka na rundunar ’yan sandan jihar Legas da ke Unguwar Yaba ya tsananta bincike domin kwato dukkanin yaran da  Misis Grace Onye ta saya a jihar.
Misis Grace ’yar asalin garin Onitsha ce, mai kimanin shekaru 52, ta shaida wa ’yan sanda cewa ta kware wajen haramtaccen kasuwancin saye da sayar da jarirai da kananan yara a Legas, inda take sayarwa ga masu bukata a yankin jihohin kabilar Igbo.
Ta  bayyana cewa ta shafe fiye da shekaru uku tana zuwa Jihar Legas domin sayan jarirai da kananan yara ta sayar, musamman ga matan da ba sa haihuwa.
An kama Misis Grace ne tare da abokiyar huldarta da ba ta haihuwa mai suna  Ngozi Ikeh ’yar kimanin shekaru 45 a duniya a unguwar Ikotun, a lokacin da suke kokarin gudu da yarinyar da suka saya a hannun mai kawo musu yara mai suna Samuel (wanda ake nema ruwa a jallo) a kan naira dubu dari uku.
Misis Grace ta kara da cewa, Samuel wanda shi ne yake sato mata yara, shi ne ya sato yarinyar ya kawo mata a otel din da ya sauke ta da ke kan titin Abiola Adeyemi a unguwar Ingando.
Binciken ’yan sanda ya gano cewa Samuel ya sato yarinya mai suna Joy Olowolade, ’yar kimanin shekaru biyu da haihuwa a gidansu da ke kan titin Oladunjoye  a unguwar Ingando  inda ya yi amfani da banga don tsorata mutanen gidan da  yarinyar take a lokacin da suke wasa a kofar gida.
‘Jim kadan da Samuel ya jefa bangar sai yaran da ke wasa a wurin suka tsorata suka tarwatse, wadansu suka yi cikin gida, wadansu kuma suka yi waje. Nan take Samuel ya yi amfani da wannan dama ya sace Joy’. Inji binciken ’yan sanda.
Dubun Misis Grace da abokiyar huldarta Ngozi ya cika ne yayin da wani makwabcin su Joy, wanda aka sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya ganta a goye a bayan Misis Grace yayin da suke kokarin sulalewa daga yankin, inda nan take ya sanar da jama’a aka kama su. Daga bisani aka mika su ofishin ’yan sanda da ke Ikotun, inda daga bisani aka kai su sashen binciken manyan laifuka na unguwar Yaba.
Iyayen yarinyar Ayodele da matarsa Funke Olowolade sun bayyana farin cikinsu dangane da samun nasarar  kwato yarinyar daga hannun wadanda suka sace ta.
’Yan sanda sun tabbatar da cewa da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da Misis Grace da Ngozi kotu a kotu.