Indiya ta harba tauraron dan Adam duniyar Mars

A shekaranjiya Laraba ne kasar Indiya ta yi nasarar harba wani tauraron dan Adam zuwa duniyar Mars, kasar ta za ma ta farko a duniya da ta yi hakan ba tare da fuskantar wani cikas ba.Tauraron dan Adam din wanda aka wa lakabi da  Mangalyaan a harshen Hindu, ya isa duniyar  Mars da safiyar Laraba […]

Indiya ta harba tauraron dan Adam duniyar Mars
Indiya ta harba tauraron dan Adam duniyar Mars

A shekaranjiya Laraba ne kasar Indiya ta yi nasarar harba wani tauraron dan Adam zuwa duniyar Mars, kasar ta za ma ta farko a duniya da ta yi hakan ba tare da fuskantar wani cikas ba.
Tauraron dan Adam din wanda aka wa lakabi da  Mangalyaan a harshen Hindu, ya isa duniyar  Mars da safiyar Laraba bayan yayi tafiyar watanni 10 daga duniyarmu ta Earth.
A baya, kasahen Amurka, da Rasha da na Turai ne kadai su ka yi nasarar aika tauraronsu duniyar ta Mars. Sai dai kasar Japan ta yi rashin nasara aike wa da shi a shekarar 2003. Hakazalika, kasar China, wadda tauraronta ita ma ya gamu da cikas a hanyarsa ta isa duniyar  ta Mars a shekarar 2011.  Kodayake, a ranar Litinin da ta gabata ne kasar  Amurka ta aika da sabon tauraronta, mai suna Maben, zuwa duniyar ta Mars.
Idan tauraron Mangalyaan ya samu tsayawa a duniyar ta Mars, zai rika daukan hotunan abubuwan da ke cikin duniyar, da kuma ba da damar yin nazari akan su.
A farkon watan nan anyi fargabar ko za a iya dogaro da aikin da tauraron dan Adam din na Indiya zai yi a duniyar Mars, ganin yadda ba a taba amfani da shi ba tun da aka harba shi daga duniyar Earth a watan Disamban bara. Amma fargabar ta kau a farkon wannan makon, bayan injiniyoyi sun tantance da kuma tabbatar da cewa duka  bangarorin tauraron suna aiki yadda yakamata.
An kaddamar da tauraron Mangalyaan daga tashar sararin samaniya ta Sriharikota a jihar Andhra Pradesh,a ranar 5 ga watan Nuwamban bara.
Kudin Indiya Rupee biliyan hudu da miliyan dari biyar ne aka kashe wajen aikin harba tauraron duniyar ta Mars, kimanin Dala miliyan 74, wanda shi ne kudi mafi karanci da aka taba kashewa a aikin harba tauraron dan Adam zuwa wata duniya. Kuma tsawon tautaron Mangalyaan bai wuce Mita daya da rabi ba.
A lokacin wani jawabi da aka yada ta gidajen talabijin, Firaminista kasar Narendra Modi, ya yaba wa injiniyoyin kasar kuma ya ce wannan nasarar abin farin ciki ce ga kowane Ba’indiye, inda ya bayyana ranar da ranar mai cike da tarihi. A karshe  ya ce “abin da masana kimiyyar kasar suka kashe wajen harba tauraron bai kai kudin da ake kashewa wajen shirya fina-finan Indiya ba.”