Indiya ta tabbatar da haramta luwadi

Kotun kolin kasar Indiya ta tabbatar da dokar da ta haramta luwadi da madigo.Kotun kolin ta soke wani hukunci da Babbar Kotun Delhi ta yanke a 2009 inda ta halatta luwadi da madigo lamarin da ka iya ba da dama a yi auren jinsi wato namiji ya auri namiji ko mace ta auri mace.A cewar […]

Indiya ta tabbatar da haramta luwadi
Indiya ta tabbatar da haramta luwadi

Kotun kolin kasar Indiya ta tabbatar da dokar da ta haramta luwadi da madigo.
Kotun kolin ta soke wani hukunci da Babbar Kotun Delhi ta yanke a 2009 inda ta halatta luwadi da madigo lamarin da ka iya ba da dama a yi auren jinsi wato namiji ya auri namiji ko mace ta auri mace.
A cewar Kotun kolin, Majalisar Dokoki ce kawai ke da damar yin doka game da lamarin.
Sashi na 377 na kundin dokokin Indiya da aka kafa shekara 153 da suka wuce a lokacin mulkin mallaka, jima’i tsakanin jinsi guda “abu ne da ya saba wa hankali” kuma akwai hukunci daurin shekara 10 ga duk wanda aka samu ya aikata haka.”
Jam’iyyun siyasa da kungiyoyin addini da na jama’a da dama sun rubuta takardun kuka ga Kotun kolin suna neman a tabbatar da dokar bayan hukuncin na shekarar 2009.
Wakilan kafafen watsa labarai sun ce duk da cewa da wuya a ce an yi amfani da dokar wajen hukunta wani kan saduwa tsakanin jinsi daya, amma ’yan sanda na amfani da ita wajen kama wadanda ake zargi da luwadi.  
 Mutanen Indiya masu tsaurin ra’ai ne da suke ganin luwadi a matsayin abin kyama, kuma mutane da dama na ganin alaka tsakanin jinsi a matsain haram.
Lokacin da yake yanke hukunci Babban Alkalin Kotun kolin Indiya Mai shari’a GS Singhbi wanda ya jagoranci alkalai biyu ya fadi a shekaranjiya Laraba wadda ita ce rana ta karshe kafin ya yi ritaya daga aiki ya ce: “Ya rage ga majalisar dokoki ta yi doka kan wannan batu. ’Yan Majalisar Dokokin suna iya duba yiwuwar shafe wannan tanadi (Sashi na 377) daga cikin doka bisa shawarar babban lauyan gwamnati.”
Ministan Shari’a na kasar Kapil Sibal ya shaida wa manema labarai cewa, gwamnati za ta girmama hukuncin, amma bai ce ko akwai shirin sauya dokar ba. Kuma manema labarai sun ce duk wata sabuwar doka zai yi wuya ta samu a kurkusa – saboda karatowar zaben kasar a badi.
Sai dai a yayin da masu rajin kare hakkin ’yan luwadi ke bakin ciki da hukuncin, kungiyoyin addini, musamman al’ummar Musulmi da Kirista sun yi maraba da hukuncin na Kotun kolin.