Indiya ta yi nasarar harba roka sararin samaniya
kasar Indiya ta samu nasarar harba kumbonta cikin sararin samaniya, wanda ta kera ta hanyar amfani da fasaha da dabarun kere-kere na cikin gida, al’amarin da ya bata damar shiga jerin kasashe masu tafiya sararin samaniya.Roka kirar Indiya, an yi mata lakabi a Turancin kimiyya da kere-kere da GSLb-D5, kuma ta cilla zuwa sararin samaniya […]

kasar Indiya ta samu nasarar harba kumbonta cikin sararin samaniya, wanda ta kera ta hanyar amfani da fasaha da dabarun kere-kere na cikin gida, al’amarin da ya bata damar shiga jerin kasashe masu tafiya sararin samaniya.
Roka kirar Indiya, an yi mata lakabi a Turancin kimiyya da kere-kere da GSLb-D5, kuma ta cilla zuwa sararin samaniya ne daga tashar Sriharikota da ke Jihar Andhra Pradesh. Don haka kasar ta shiga cikin jerin manyan kasashen duniya, wadanda suka kware a wannan fasahar kere-kere da harba kumbo duniyoyin sama.
An sha daga wajen kere wannan roka da harba, inda kasa harbata tun cikin watan Agustan bara. A wannan karon Cibiyar Binciken Sararin Samaniya ta Indiya (ISRO), ta harba roka mai nauyin ton 415, a karkashin jagorancin Dokta K Radhakrishnan. Tsawon shekaru kasar ta shafe ta kokarin zuwa sararin samaniya. Kuma rokar farko da Indiya ta kera ta yi hadari ne a watan Afrilun 2010.