Indiya za ta saki mutanen da aka yanke wa hukuncin kisan Rajib Gandhi
Gwamnatin Tamil Nadu da ke kasar Indiya za ta saki mutum bakwai da ka kama su da laifin kashe tsohon Firayiministan kasar Rajib Gandhi, a shekarar 1991.Jaridar The Guardian, ta ruwaito cewa an yanke wannan hukuncin ne kwana daya da Kotun kolin Indiya, ta mayar da hukuncin kisan ya zama zaman kurkuku na rai da […]
Gwamnatin Tamil Nadu da ke kasar Indiya za ta saki mutum bakwai da ka kama su da laifin kashe tsohon Firayiministan kasar Rajib Gandhi, a shekarar 1991.
Jaridar The Guardian, ta ruwaito cewa an yanke wannan hukuncin ne kwana daya da Kotun kolin Indiya, ta mayar da hukuncin kisan ya zama zaman kurkuku na rai da rai, a kan mutum ukun.
Alkalai sun yanke musu hukunci a shekara 20 da suka gabata, amma an kasa gane dalilan da suka sanya aka kasa aiwatar da hukuncin kisa a kansu; kuma rashin aiwatarwar na tsawon wannan lokaci cutarwa ce gare su. Wata rana kuma sai gwamanti ta yi tunanin cewa zaman wakafi na shekara 20 ya isa haka.
Rajib Gandi, wanda da ne ga Indira Gandhi, kuma jika a wajen dan gwagwarmayar kwatar ’yancin Indiya, Mahtma Gandhi. An halaka shi ne a shekarar 1991.