Indiyawa na bauta wa akuya mai fuskar mutum
Bayan haifar wata akuya ’yan kwanaki kadan a garin Rajasthan da ke Arewa maso Yamma a kasar Indiya, tuni wadansu suka fara bauta mata. Akuyar da take da fuskar mutum tana tsorata jama’ar yankin. Mazauna garin da akuyar take suna bauta mata a matsayin wadda suke neman abin duniya daga gare ta. Jama’ar garin Nimodia […]
Bayan haifar wata akuya ’yan kwanaki kadan a garin Rajasthan da ke Arewa maso Yamma a kasar Indiya, tuni wadansu suka fara bauta mata.
Akuyar da take da fuskar mutum tana tsorata jama’ar yankin.
Mazauna garin da akuyar take suna bauta mata a matsayin wadda suke neman abin duniya daga gare ta.
Jama’ar garin Nimodia a Jihar Rajasthan, sun yi matukar mamakin bayyanar wannan dabbar mai fuska irin ta mutane da idanu, kamar ba akuya ba.
Wanda ya mallaki akuyar mai suna Mukeshji Prajapap, ya ce, akuyar tana fama da wata cuta mai suna “cyclopia” da ta haddasa irin wannan sura. Kuma cutar tana iya haddasa sauya kamar dabbar ta asali.
Rahotanni sun ce wadansu mazauna kauyen Nimodia na ci gaba da bauta wa wannan akuya.
Wani lokaci a kasar Indiya ana samun sauyin halittar dabbobi sukan dauki hankalin jama’a da dama.
Wasu kafafen sadarwa na shafukan Intanet sun wallafa yanayin halittar akuyar lokacin da take motsi da jelarta.
Rahoto ya bayyana cewa, a duk cikin dabbobi dubu 16 ana iya samun daya wadda take da irin wannan cuta ta cyclopia kuma za ta iya cutar da dan Adam.
A watan da ya gabata a kasar Ajentina, an samu wata saniya da ta haifi jaririya mai hanci da baki irin na mutum. Likitocin dabbobi sun yi bakin kokarinsu, amma daga bisani bayan wasu awanni ta mutu a garin Billa Ana da ke Areawancin kasar.
A watan Nuwamba bara a kasar China, an samu rahoton bayyanar wani kifi da ke da fuskar mutum da hanci da kuma idanu biyu.