Indiyawa sun kirkiro takalma masu nuna hanya da kiddige nisan tafiya

Wani Kamfanin kere-kere na kasar Indiya, Ducere Technologies, ya kirkiro takalaman GPS, da idan aka ba su umarni za su rika nuna wa mutum hanya, sun kididdige yawan tattakin da mutum ya yi da nisan tafiya, tare kona makamashin jiki. Za a fara sayar da takalaman a cikin wannan watanWadannan takalaman motsa jiki, an yi […]

Indiyawa sun kirkiro takalma masu nuna hanya da kiddige nisan tafiya
Indiyawa sun kirkiro takalma masu nuna hanya da kiddige nisan tafiya

Wani Kamfanin kere-kere na kasar Indiya, Ducere Technologies, ya kirkiro takalaman GPS, da idan aka ba su umarni za su rika nuna wa mutum hanya, sun kididdige yawan tattakin da mutum ya yi da nisan tafiya, tare kona makamashin jiki. Za a fara sayar da takalaman a cikin wannan watan
Wadannan takalaman motsa jiki, an yi musu lakabin sunan “LeChal,” wanda a Harshen Hindi na nufin “dauke ni ka kaini.” Takalaman “LeChal,” wadanda jajaye ne, suna tare da masarrafan wayar salula da suka hada da Bluetooth, wadanda ke taimaka wa matafiyi samun taswirar wurare, kamar yadda shafin sadarwar Google ya tsara, sannan ya bai wa mutum umarnin bin hagu, ko dama.
Wanda ya kirkiro wadannan takalama, shi ne Krispian Lawrence da Anirudh Sharma, wadanda shekarunsu ba su wuce 28 ba, kuma Injiniyoyi ne da suka kammala karatu, suka kamfaninsu na kashin kansu, mai suna Ducere. Sun kafa kamfanin ne a wadani dan karamin gida, a shekarar 2011, inda suka samu masu saka hannun jari, har ta kai ga sun dauki mutum 50 aiki.
“Mun yi tunanin yin wannan kirkira ne domin zai taimaka wa nakasassu, kuma zai yi aiki ne ba tare da wata kara ta damu mutum ba,” a cewar Lawrence lakacin da yake ganawa da manema labarai.