Indiyawa sun koma wanka da kashin shanu saboda Coronavirus
Babu wata shaida da ke nuna kashin shanu na kara inganta garkuwar jiki.
Likitoci a kasar Indiya sun bukaci mutane su daina mulke jikinsu da kashin shanu a kokarinsu na yaki da cutar Coronavirus.
Jami’an kiwon lafiya sun ce babu wata shaida a kimiyyance da ta amince da wannan abu da Indiyawa suke yi, inda suka yi gargadin hakan na iya yada wasu cututtuka.
- ‘Buhari ya fi shekara 40 yana zuwa Landan a duba lafiyarsa’
- An kashe makiyaya 6 a Taraba —’Yan sanda
Wannan abu yana zuwa ne a daidai lokacin da kasar Indiya take dada fuskantar daukin gaggawa a bangaren kiwon lafiya, inda sama da mutum miliyan 22 da dubu 660 suka harbu da cutar Coronavirus, kuma mutum dubu 246 da 116 aka samu rahoton cutar ta kashe.
A yayin da kwararru suke cewa gaskiyar adadin wadanda suka kamu ko suka rasu yana iya ninka abin da aka bayar da rahotonsa sau biyar ko sau goma.
Majinyata a sassan kasar suna fuskantar mugun karancin gadajen kwanciya a asibitoci da iskar taimaka wa numfashi da magunguna, lamarin da yake jawo mutane da dama su mutu a dalilin rashin yi musu jinya.
A Jihar Gujarat da ke yammacin kasar, wadansu mutane sun koma shingayen shanu suna shafe jikinsu da kashin shanun da fitsarinsu akalla sau daya a mako, bisa fatar za su kara musu garkuwar jiki ko su taimaka musu su farfado daga cutar.
A Indiya dai saniya aba ce mai tsarki, inda take zama alami na rayuwa a addinin Hindu.
An dauki karnoni mabiya addinin Hindu suna amfani da kashin saniya wajen tsarkake gidajensu da kuma yin bauta da su, bisa tsammanin tana da wasu mu’ujizoji.
Wani karamin manaja a wani kamfanin harhada magunguna mai suna Gautam Manilal Borisaya yi da’awar cewa shafe jikinsa da kashin shanun ya taimaka masa wajen warkewa daga Coronavirus a bara.
Ya ce, “Mun gani… hatta likitoci sukan zo nan.
Sun yi imanin cewa wannan tsari yana karfafa garkuwar jikinsu kuma sukan koma su kula da masu cutar ba tare da tsoro ba.”
Mista Borisa yana yawan zuwa Shree Swaminarayan Gurukul Bishwabidya Pratishthanam, wata makaranta da wasu limaman addinin Hindu suke tafiyarwa a kusa da hedkwatar Zydus Cadila, wadda take kokarin kirkiro nata alluran rigakafin cutar.
A daidai lokacin da mutanen suke jiran kashin shanu da fitsarinsu da aka gauraya suka mulke jikinsu su bushe, sukan rungumi shanu ko su girmama su a dakunansu.
Sannan su yi wasan Yoga don karfafa kwarin jikinsu bayan nan sai a wanke da madarar shanun.
Sai dai likitoci a sassan duniya sun sha nanata yin gargadi cewa har yanzu ba a samu wani magani na magance cutar Coronavirus baya ga allurar riga-kafi, suna masu cewa irin wadannan abubuwa suna iya zama karya da barazana ga kiwon lafiya.
Shugaban Kungiyar Likitoci ta Kasar Indiya, Dokta JA Jayalal, ya ce: “Babu wata kwakkwarar shaida a kimiyance da ke nuna kashin shanu ko fitsarinsu za su iya kara inganta garkuwar jiki don yaki da cutar Coronavirus, wannan kawai camfi ne.
“Akwai barazana ga kiwon lafiya a rika shafe jiki ko a ci wadannan abubuwa – za a iya yada wasu cututtuka daga dabbobin zuwa ga mutane,” inji shi