Indiyawan da ke bautar mace mai taɓin hankali
Galibi tana yin watsi da masu bautarta kuma ba alamar ta fahimci cewa ana bauta mata.
Wata mai suna Topi Amma, ma’abociyar sa hula mai malafa da ke garin Tiruvannamalai, birnin da mabiya Hindu ke zuwa don ibada a Jihar Tamil Nadu, tana kawo ruɗani a cikin addini, inda ta raba kan wasu Indiyawa wasu na bauta mata wasu na ɗaukarta a matsayin mahaukaciya da take neman taimako.
Indiyawa suna da nasu irin sufayen da yawa, saboda suna da abubuwan bauta na Hindu da mutane ke tururuwar zuwa, amma lamarin Topi Amma abu ne mai wuyar fahimta.
- Ya gano amaryarsa namiji ne bayan kwana 12 da aurensu
- Sarautar Kano: Yadda ’yan siyasa ke gwara kan ’yan uwa
Ana yawan kiran Topi da ‘sidha’, wato wata halitta mai wayewa wacce ta samu kamala. Amma ga wasu, mace ce mai naƙasa da take buƙatar taimakon likita.
A Indiya idan mabiya addini suka ga wani sufi yana tafiya a titunan garin Tiruɓannamalai kuma yana magana da harshen Tamil na da wanda ba wanda ke fahimta, sai su fara tsarkake shi.
Idan kuma suka ga mutum na yawo, babu gaira babu dalili musamman mace sai su fara tsarkake ta.
Sai dai duka hasashe ne, domin idan aka yi la’akari Topi Amma, ba ma sha’awar addini take ba.
Rayuwar Topi, kafin ta shahara a garin Tiruvannamalai har ta jawo hankalin ɗimbin mabiya, ta kasance a ɓoye, amma sai cikin ƙanƙanin lokaci ta fara shahara.
Bayanai sun ce matar ba ta iya haɗa jimloli biyu masu ma’ana, kuma da wuya ta yi ƙarin haske a kan wani batu, amma duk da hakan ana samun masu yaɗa labarai a kanta don ƙara nuna shahararta.
Shafukan Intanet cike suke da gajerun faifan bidiyo na mutanen da suke zuwa wajen Topi Amma a Tiruɓannamalai, kuma ko dai suna biye da ita yayin da take tafiya a cikin birnin, yayin da wasu ke ɗauko kofuna don ta yi musu tofi a ciki su samu tabarrukinta.
Abu ne mai ban al’ajabi, idan aka yi la’akari da cewa matar ta yi kama da mai taɓin hankali mara gida da ke sanye da tufafi masu ƙazanta, mai yiwuwa ba ta yin wanka, kuma ga alama tana cikin ɗimuwa, amma wasu na ɗaukarta abin bauta.
“Ana bauta wa mace mai taɓin hankali ‘Thoppi Amma’ a cikin garin Tiruɓannamalai,” wani mutum da ya yaɗa bidiyo na sufanci ya rubuta a shafinsa na sada zumunta na X (Twitter).
Amma ba mutumin da ya isa ya ce, tana fama da taɓin hankali kuma tana buƙatar taimako.
Mutane da yawa suna rera mata baitukan yabo suna fassara mata duk wani aiki na rashin hankali a matsayin abin bautarsu kuma mai cike da manufa.
Abin ban mamaki, saboda naƙasar tunaninta, Topi Amma galibi tana yin watsi da masu bautarta kuma ba alamar ta fahimci cewa ana bautarta a matsayin cikakkiyar halitta take da ikon sihiri.
Haka kawai a yini, sai a ga cincirindon jama’a na bin ta kusan duk inda ta je.