INEC ta ba Adeleke takardar shaidar lashe zaben Gwamnan Osun
An gudanar da bikin ne a Osogbo, babban birnin jihar
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ba Sanata Ademola Adeleke takardar shaidar lashe zaben Gwamnan da aka yi a jihar Osun.
Hukumar ta mika masa takardar ne a ranar Laraba a Osogbo babban birnin jihar.
- An hana sarakunan Zamfara ba da kowacce irin sarauta sai da amincewar Gwamna
- An yi wa matashiya fyade sannan aka kashe ta a Edo
Adeleke wanda ya tsaya zaben a karkashin jam’iyyar PDP ya doke abokin takararsa, kuma Gwamna mai ci, Gboyega Oyetola na jam’iyyar APC, wanda ya ke neman wa’adi na biyu kan karagar mulkin jihar.
Tun farko dai fitaccen mawakin nan na Kudancin Najeriya, David Adeleke wanda aka fi sani da Davido, ne ya tayar da kura kan cewa INEC ba ta bai wa Adeleke, wanda kawunsa ne takardar shaidar lashe zaben ba, kwanaki biyu da kammala shi.
Yayin da ya ke mayar da martani kan lamarin, daya daga cikin Kwamishinonin hukumar zaben ta kasa, kuma shugaban kwamitin yada labari da wayar da kan a jama’a, Festus Okoye, ya ce hukumar na da mako biyu bayan zabe ta ba wanda ya ci takardar shaida.
Ya na mai cewa, “Farfesa Kunle Ajayi, kwamishinan zabe na kasa mai kula da jihohin Ogun da Ondo, da Osun, yana cikin jihar kuma a ko wane lokaci zai ba wanda ya lashe zaben takardar shaida a ranar Laraba.”
Sashe 71 (1) na dokar zabe ta kasa na shekarar 2022, ya ba hukumar zaben damar ba duk wanda ya lashe zabe takardar shaidar lashe zaben kwana 14 bayan gudanar zaben.