INEC ta ba Fintiri shaidar lashe zaben Gwamnan Adamawa

Ya karbi shaidar ce a hedkwatar hukumar da ke Abuja

INEC ta ba Fintiri shaidar lashe zaben Gwamnan Adamawa

Ahmadu Fintiri

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ba Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri shaidar lashe zaben Gwamnan Jihar a karo na biyu.

INEC ta ba Fintirin shaidar ce a Abuja, kwana daya bayan ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben da ta bayyana sakamakonsa.

Gwamna Fintiri ya karbi shaidar ce tare da mataimakinsa, Farfesa Kaletapwa Farauta, wajen misalin karfe 5:00 na yammacin Laraba a hedkwatar hukumar ta kasa da ke Abuja.

Ya sami nasarar ce a karkashin jam’iyyar PDP, bayan ya lashe zaben da ya sha fama da dambarwa iri-iri, inda ya kayar da babbar abokiyar hamayyarsa ta jam’iyyar APC, Sanata Aisha Dahiru Binani.

A karshen zaben dai, ya sami kuri’a 430,861 ne, inda ita kuma Binani ta sami kuri’a 398,738.