INEC ta ba zababben Gwamnan Bayelsa shaidar nasarar zabe

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bai wa zababben Gwamnan jihar Bayelsa David Lyon, da Mataimakinsa Sanata Degi Eremienyo, takardar shaidar cin zaben jihar da aka yi. Hukumar INEC ta mika takardar shaidar ne tare da Dan Majalisafr Dokokin jihar Dakta Charles Daniel, a yau Alhamis. Kwamishinar zabe ta shiyyar jihohin Ribas, […]

INEC ta ba zababben Gwamnan Bayelsa shaidar nasarar zabe

David Lyon

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bai wa zababben Gwamnan jihar Bayelsa David Lyon, da Mataimakinsa Sanata Degi Eremienyo, takardar shaidar cin zaben jihar da aka yi.

Hukumar INEC ta mika takardar shaidar ne tare da Dan Majalisafr Dokokin jihar Dakta Charles Daniel, a yau Alhamis.

Kwamishinar zabe ta shiyyar jihohin Ribas, Bayelsa da Edo Misis May Agbamuche-Mbu, ce ta mika takardar shaidar ga zababben Gwamnan da Mataimakinsa.