INEC ta bayyana Shekarau a matsayin wanda ya lashe kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya

Duk da Shekarau ya sanar da ficewarsa daga NNPP, INEC ta ce shi ta sani a matsayin dan takara

INEC ta bayyana Shekarau a matsayin wanda ya lashe kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar da sunan Ibrahim Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Kano ta tsakiya a karkashin Jam’iyyar NNPP.

Baturen zaben Farfesa Tijjani Hassan Darma ne ya bayyana Sanata Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’a 456,787 akan babban abokin karawarsa na Jamiyyar APC Abdulkarim Abdussalam Zaura wanda ya sami kuri’a 168, 677.

Idan za a iya tunawa Sanata Ibrahim Shekarau shi ne wanda Jam’iyyar NNPP ta fara tsayarwa a matsayin dan takararta a kujerar sanatan Kano ta Tsakiya kafin daga bisani ta maye gurbinsa da Sanata Rufa’i Sani Hanga sakamakon barin Jamiyyar ta NNPP da Shekarau din ya yi.

Lamarin da ya jefa mutane da yawa cikin rudani, inda magoya bayan jam’iyyar ta NNPCL suke cewa ba za ta sabu ba.