INEC ta cire sunan Ahmad Lawan daga jerin ’yan takarar 2023

INEC ta ce ba a kawo mata bayanan wanda zai yi takarar Sanatan a Mazabar da Ahmad Lawan ke wakilta ba.

INEC ta cire sunan Ahmad Lawan daga jerin ’yan takarar 2023

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta cire sunan Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan daga jerin ’yan takarar zaben 2023 da Jam’iyyar APC mai mulki ta mika mata.

Hukumar ta kuma cire sunan Ministan Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio da Gwamnan Jihar Ebonyi, Dave Umahi, wadanda su ukun sun nemi takarar shugaban kasa a jam’iyyar, amma da ba su kai labari ba, suka nemi komawa takarar Sanata, matakin da ya bar baya da kura.

Da yake bayani kan jerin sunayen ’yan takarar da INEC ta fitar ranar Juma’a, Kwamishinan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a na hukumar, Barista Feature Okoye, ya ce, “Idan jam’iyya ta mika wa INEC sunan wani dan takara da ba ta hanyar sahihin zaben fitar da dan takara aka zabe shi ba, to bai zama dole ba INEC ta wallafa sunansa.”

Ya ci ga da cewa, “Duk wani dan takara da INEC ba ta wallafa sunansa ko bayanansa ba a yau (Juma’a), to abin nufi shi ne ba ta sahihin zaben fitar da dan takarar jam’iyyar aka tsayar da shi ba.”

Ya bayyana cewa babu wata doka da ta wajabta wa INEC wallafa sunayen ’yan takarar da ba ta hanyar sahihin zaben fitar da ’yan takara aka zabe su ba.

Idan ba a manta ba, Aminiya ta kawo rahoto a kwanakin baya cewa bayan faduwar Ahmad Lawan a zaben dan takarar shugaban kasa, akwai yiwuwar zai yi biyu babu, bayan mutumin da ya lashe zaben dan takarar Mazabar Yobe ta Arewa, Bashir Machina, ya ki ya janye mishi.

Bayan matsin lamba da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Jihar Yobe suka yi wa Machina domin ya janye wa Ahmad Lawan, sai ya  rubuta wa INEC yana gargadin ta game da duk wani yunkuri na maye gurbinsu da wani.

Sai dai kuma daga baya Jami’yyar APC ta mika wa INEC sunan Ahmad Lawan a matsayin dan takarar kujerar.

APC ba ta da dan takara a kujerar Ahmad Lawan

Amma wasu majiyoyi daga Hukumar INEC reshen Jihar Yobe sun bayyana cewa APC ba ta da dan takarar kujerar Sanatan Yobe ta Arewa, mazabar Ahmad Lawan da Machina a zaben 2023.

Majiyoyinmu sun ce daga Ahmad Lawan har Bashir Machina babu wanda hukumar ta wallafa sunansa a matsayin dan takarar Sanatan Yobe ta Arewa.

“Mun karbi sunan Mohammed Bomoi a matsayin dan takarar Sanatan Yobe ta Kudu sai kuma Ibrahim Geidam a matsayin dan takarar Sanatan Yobe ta Gabas, amma babu sunan dan takarar Sanatan Yobe ta Arewa na Jam’iyyar APC,” a cewar majiyar.

Shugabar Sashen Wayar da Kai da Hulda da Jama’a ta Ofishin INEC na Jihar Yobe, Rifkatu Duku, ta bayyana cewa ba a mika wa Hedikwatar hukumar takardun dan takarar Sanatan Yobe ta Arewa ba.

Ta ce, “An kawo mana bayanan ’yan takarar Majalisar Dokoki ta Kasa da na Shugaban Kasa; Amma ba a kawo mana na Sanata mai wakiltar Yobe ta Arewa ba, duk da cewa mun samu na Yobe ta Kudu, Ibrahim Bomoi da kuma tsohon Gwamnan Jihar Yobe Ibrahim Gaidam.”

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi