INEC ta dakatar da jami’inta kan batan sakamakon zabe a Filato
Hukumar ta ce tuni jami’an tsaro suka fara gudanar da bincike.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta dakatar da jami’in zaben Karamar Hukumar Jos ta Arewa, Mista Fred Ogboji, kan bacewar sakamakon zaben cike gurbi da aka gudanar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban sashen ayyukan zabe na jihar, Mista Isah Idakwo, ya fitar a ranar Lahadi.
“An dakatar da kai don samu damar gudanar da bincike kan batan sakamakon zaben ‘yan majalisar wakilai a rumfuna 16.”
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito yadda INEC ta gudanar da zaben cike gurbi a mazabu 16 na mazabar Jos ta Arewa.
Shugaban Hukumar Zaben jihar, Dokta Oliver Agundu, ya sanar da dage zaben cike gurbin zuwa ranar Lahadi 4 ga watan Fabrairu.
Agundu ya ce za a fara kada kuri’a da misalin karfe 9:30 na safe zuwa karfe 3:30 na yamma.
Shugaban ya bayyana cewa hukumar ta gano sakamakon zaben rumfuna 16 na mazabar Jos ta Arewa da Bassa sun yi batan dabo a ranar Asabar bayan kammala zaben.
Ya ce an mika lamarin ga jami’an tsaro domin gudanar da binciken kan yadda sakamakon ya bace.