INEC ta dakatar da tattara sakamakon Adamawa

An sanar da Binani a matsayin wacce ta yi nasara tun ba a gama ƙidaya ƙuri’un da aka kaɗa ba.

INEC ta dakatar da tattara sakamakon Adamawa

Hukumar Zabe ta Kasa, INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaben gwamnan Jihar Adamawa bayan da Kwamishinan Zabe ya yi azarɓaɓin sanar da sakamakon kafin kammala ƙidaya kuri’u.

Kwamishinan hulɗa da jama’a da wayar da kan al’umma na INEC, Barista Festus Okoye ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter.

Barista Okoye ya ce INEC ta dakatar da tattara sakamakon ne bayan da Kwamishinan Zabe na Jihar Adamawa, Hudu Yunus Ari ya sanar da Aishatu Ɗahiru Binani ta APC a matsayin wacce ta yi nasara tun ba a gama ƙidaya ƙuri’un da aka kaɗa ba.

Ya ce sanar da sakamako aikin Jami’in Tattara Sakamako ne ba wai Kwamishinan Zaɓe ba.

Don haka sanarwar Kwamishinan Zaɓen ba ta da wani tasiri a doka.

Haka kuma, INEC ta gayyaci Kwamishinan Zaɓen, da Jami’in Tattara Sakamakon, da duk  masu ruwa-da-tsaki zuwa hedkwatarta da ke Abuja domin gano bakin zaren.