INEC ta dakatar da zaɓe a jihohi 3 saboda tarzoma

Tarzoma ta barke a jihohin Kano, Akwa Ibom da Enugu

INEC ta dakatar da zaɓe a jihohi 3 saboda tarzoma

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta dakatar da zaɓukan cike gurbi da take gudanarwa yau Asabar a wasu mazabu da rumfunan zabe na jihohin Kano, Akwa Ibom da Enugu sakamakon tarzoma da ta barke.

Mista Sam Olumekun, kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, shi ne ya bayyana hakan a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da zaɓen cike gurbi a jihohi 26 da kananan hukumomi 80 da abin ya shafa.

Ya bayyana cewa an dakatar da zaɓen a Jihar Akwai sakamakon arcewa da kayayyakin zaɓe da wasu masu tayar da zaune tsaye suka yi a wasu rumfunan zaɓe na kananan hukumomin Ini da Ikono.

A Jihar Enugu kuma, an dakatar da zaɓen ne a dukkan rumfunan zaɓe takwas na Karamar Hukumar Enugu ta Kudu 1 a dalilin bayyanar takardun sakamakon zaɓe tun gabanin masu zaɓe su soma kaɗa kuri’a.

Hakazalika, a zaɓen mazabar Kunchi da Tsanyawa da ke Jihar Kano, an dakatar da zaɓen a dukkanin rumfunan zaɓe guda 10 sakamakon yadda wasu ’yan daba da suka tayar da tarzoma hana gudanar da zaɓen cikin daɗin rai.

Mista Olumekun ya ce hukuncin dakatar da zaɓukan ya yi daidai da tanadin sashe na 24 (3) na Dokar zabe, inda zuwa ranar Litinin INEC za ta sanar da ɗaukar matakan da suka dace dangane da mazabun da abin ya shafa.

Ya yi kira ga jami’an tsaro da su binciki lamarin, yayin da ya ce Hukumar INEc ta yi alkawarin gudanar da nata binciken kan duk jami’anta da aka ɗora wa alhakin gudanar da zaɓen.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja