INEC ta fitar da jadawalin zaben 2019

A ranar Talatar da ta gabata ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa, INEC ta fitar da jadawalin zaben kasar nan na shekarar 2019. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya shaida wa manema labarai hakan a Abuja, inda ya ce za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin […]

INEC ta fitar da jadawalin zaben 2019

A ranar Talatar da ta gabata ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa, INEC ta fitar da jadawalin zaben kasar nan na shekarar 2019. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya shaida wa manema labarai hakan a Abuja, inda ya ce za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin tarayya ranar Asabar, 16 ga Watan Fabrairu.

Sai kuma zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da kuma na birnin tarayya wanda za a gudanar da su a ranar biyu ga watan Maris. Farfesa Yakubu ya ce daga yanzu za a rika gudanar da zabukan ne a ranakun da aka ayyana ba tare da an dagewa ko jinkirta gudanar da su ba.

Ya ce za a kammala zabukan fitar da gwani da kuma warware korafe-korafen da za su biyo bayansu kafin ranar 18 ga Watan Agustan 2018. Sannan hukumar ta umarci jam’iyyun siyasa da su tabbatar sun kammala zabukan cikin gida na fitadda gwani kafin ranar bakwai ga Watan Oktobar wannan shekarar. 

daruruwan ‘yan takara daban-daban daga jam’yyu 67 da hukumar zaben ta yi wa rajista ne dai ake ganin za su fafata a zabukan cikin gidan wajen neman kujerar shugaban kasa, gwamnoni, ‘yan majalisar tarayya da na jihohi. 

Sannan kuma shugaban hukumar zaben ya ce ba za a amince da fara yakin neman zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya ba, har sai zuwa ranar 18 ga Watan Nuwambar wannan shekarar. Sannan karshe na tsaida yakin neman zaben shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya zai kasance ranar 14 ga Watan Fabrairun 2019 yayin da ranar karshe na yakin neman zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi zai kasance ranar 28 ga watan Fabrairu.