INEC ta fitar da ranakun zabukan 2023

INEC ta ce za a yi zaben Shugaban Kasa ranar 25 ga Fabrairun 2023.

INEC ta fitar da ranakun zabukan 2023

Shugaban Hukumar Zabe ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu

Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta sanar da ranakun da za a gudanar da zabukan shekara ta 2023 masu zuwa.

Shugaban Hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu ne ya sanar da hakan a Abuja lokacin yake yi wa ’yan jarida jawabi.

A cewarsa, za a gudanar da zaben Shugaban Kasa da na ’yan majalisar tarayya ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, yayin da za a gudanar da zaben Gwamnoni da na ’yan majalisun jihohi ranar 11 ga watan Maris na shekarar.

Farfesa Mahmud ya ce, “Za a yi zaben Shugaban Kasa da na ’yan majalisar tarayya ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

“Na Gwamnoni da ’yan majalisun jihohi ranar 11 ga watan Maris din 2023. Daga yau [Asabar] ke nan, saura kwana 365 babban zaben 2023,” inji Farfesa Mahmud.

Shugaban na INEC ya kuma ce za a fara yakin neman zaben Shugaban Kasa daga ranar Laraba, 28 ga watan Satumban 2022, sai kuma na Gwamnoni da za a fara daga 12 ga watan Oktoban 2022.

Hukumar ta kuma ce za a kammala yakin neman zaben Shugaban Kasa ranar 23 ga watan Fabrairun 2023, sai kuma na Gwamnoni ranar tara ga watan Maris din 2023.