INEC ta sanar da ranar da za a yi zaben 2019
Hukumar zaben Najeriya INEC ta sanar da ranar 16 ga watan Fabrailun 2019 a matsayin ranar da za a yi zaben Shugaban Kasa mai zuwa da na Majalisun Tarayya kamar yadda Premium Times ta ruwaito. Hakanan kuma hukumar ta sanar da cewa za a yi zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da na yankunan […]

Hukumar zaben Najeriya INEC ta sanar da ranar 16 ga watan Fabrailun 2019 a matsayin ranar da za a yi zaben Shugaban Kasa mai zuwa da na Majalisun Tarayya kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Hakanan kuma hukumar ta sanar da cewa za a yi zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da na yankunan Babban Birnin Tarayya Abuja a ranar biyu ga watan Maris na shekarar.
Hukumar ta kumsa sanar da cewa za a fara zabukan fidda gwani ne daga watan Agusta na bana, sannan kuma za a fara yakin neman zaben Shugaban Kasa daga 18 ga watan Nuwamba, yayin da za a fara na gwamnoni da ‘yan majalisan jiha a ranar 1 ga watan Disamba na 2018.