INEC ta soma tattara sakamakon Zaɓen Gwamnan Edo

INEC ta ce za ta karɓi sakamakon zaɓen ne da suka fito daga ƙananan hukumomi ba daga nau’urar IREV ba.

INEC ta soma tattara sakamakon Zaɓen Gwamnan Edo

Hukumar Zaɓe ta Kasa INEC ta soma aikin karɓa da tattara sakamakon Zaɓen Gwamnan Jihar Edo da aka gudanar ranar Asabar.

Shugaban Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Minna, Farfesa Farouk Adamu Kuta ne babban jami’in tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar.

Babbar Jami’ar INEC ta ƙasa da ke kula da zaɓen, Farfesa Rhoda Gumus ta ce a halin yanzu akwai sakamakon ƙananan hukumomi 14 zuwa 15 a zauren tattara sakamakon.

Ta kuma ce za su yi amfani da bayanan da suka fito daga ƙananan hukumomi ne kawai ba daga na’urorin IREV ba duk da cewa komai ya kammala a IREV ɗin.

A sakamakon farko wanda ya kasance na Ƙaramar Hukumar Igueben da INEC ta tattara, jam’iyyar PDP ce ta yi nasara bayan samun ƙuri’u 8,470 yayin da APC da ke biye da ita ta samu ƙuri’u 5,907.

Tun farko dai jam’iyyar PDP mai mulki a jihar ta buƙaci INEC da ta bayyana sakamakon zaɓen da ke kan na’urorin adana sakamakon zaɓe na hukumar wato IREV.

Gwamna Godwin Obaseki da takwarorinsa na Adamawa da Taraba ne suka bayyana haka a wani taron manema labarai da suka gabatar a ɗakin tattara sakamakon zaɓe na jam’iyyar wato ‘PDP Situation Room’.

Gwamnonin uku sun zargi INEC da rubuta sakamakon da ba na gaskiya ba a kan takardar rubuta sakamakon a wasu rumfunan zaɓen jihar.

Tuni dai INEC ta ce ƙaddamar da bincike kan zargin rubuta sakamakon bogin a kan takardun rubuta sakamakon zaɓen.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano