INEC ta wallafa sakamakon zabe 66,600 a shafin iRev

Wannan ci gaba ne, sabanin zaben shugaban kasa, wanda aka samu jinkirin sanya sakamakon a iRev.

INEC ta wallafa sakamakon zabe 66,600 a shafin iRev

Kawo yanzu, Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanya sakamako sama da 66,634 na zaben gwamnoni da ’yan majalisar dokokin jiha da aka gudanar ranar Asabar a shafin tattaara sakamakon zabe na iReV.

Zuwa lokacin kammala wannan labari, INEC ta sanya sakamako 66,634 a shafin, daga jihohi 28 da aka yi zaben na ranar Asabar.

Wannan wani ci gaba ne, sabanin zaben shugaban kasa da ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, wanda aka samu jinkirin sanya sakamakon a iRev.

iRev shi ne  shafi na musamman da INEC ta tanada domin wallafa sakamako tun daga rumfar zabe, ta hanyar amfani da na’urar tantance masu zabe ta BVAS, bayan jami’an zabe da wakilan jam’iyyu sun sanya hannu a kan takardar sakamakon.

Tsaikon da aka samu a wancan karon ya haifar da surutai a yayin da jam’iyyun adawa suka ki karbar uzurin hukumar game da tangardar da shafin ya samu.

Hasali ma, sun bukaci a soke zaben gaba daya, ko da yake INEC ta yi watsi da bukatar.