INEC ta yi alkawarin magance matsalolin zabe

Hukumar Zabe ta kasa (INEC) a Jihar Katsina ta ce, za ta yi bakin kokarinta don ganin ta magance matsalolin da ake kuka da su kafin gudanar da zaben badi. Kwamishinan Hukumar ta Jihar Alhaji Abubakar Umar Wara ya fadi haka a yayin da yake mayar da jawabi ga Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Dokta […]

INEC ta yi alkawarin magance matsalolin zabe
INEC ta yi alkawarin magance matsalolin zabe

Hukumar Zabe ta kasa (INEC) a Jihar Katsina ta ce, za ta yi bakin kokarinta don ganin ta magance matsalolin da ake kuka da su kafin gudanar da zaben badi. Kwamishinan Hukumar ta Jihar Alhaji Abubakar Umar Wara ya fadi haka a yayin da yake mayar da jawabi ga Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Dokta Mustafa Inuwa lokacin da shugabannin jam’iyyar suka kai masa ziyara a ranar Talata.
Kwamishinan ya ce, sai da hadin kai a tsakanin hukumar da jam’iyyun siyasa za a iya samun nasarar gudanar da zabe, kuma hukumarsa za ta yi kokari wajen raba katunan zabe na dindindin tare da ci gaba da yin rajistar masu zabe. Kwamishinan ya ce hukumar za ta yi aiki kafada-da-kafada da jam’iyyun a jihar, kuma ya bukaci jam’iyyun su fadakar da magoya bayansu, su fito don karbar katunan zabe tare da yin rajista don ba su damar jefa kuri’a a zaben badi.
Tun farko, Dokta Mustafa Inuwa ya shaida wa Kwamishinan cewa, sun ziyarci hukumar ne don nuna goyon bayansu ga hukumar ta yadda za a samu nasarar gudanar da harkokin da suka shafi zabe a jihar.