INEC za ta sake zaben dan majalisa a mazabar Alhassan Doguwa

INEC ta ce babu wanda ya lashe zaben kujerar Majalisar Tarayya ta Doguwa Tudun Wada.

INEC za ta sake zaben dan majalisa a mazabar Alhassan Doguwa

Alhassan Ado Doguwa

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta soke zaben kujerar dan Majalisar Tarayya da aka gudanar a wasu rumfunan zabe 13 a Karamar Hukumar Tudun Wada ta Jihar Kano.

Hukumar ta kuma ba da umarni a ranar Alhamis cewa a sake zaben da aka gudanar a wuraren, kafin daga baya a sanar da wanda ya yi nasara.

Baturen zaben kujerar dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Doguwa da Tudunwada, Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai, ya sanar cewa babu wanda ya lashe zaben kawo yanzu.

Hakan kuwa na zuwa ne a ranar da INEC ta mika wa zababbun sanatoci da ’yan majalisar Tarayya takardun shaidar cin zaben 2023.

Da farko INEC ta ayyana Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Tarayya, Alhassan Ado Doguwa, a matsayin wanda ya yi nasara a zaben, kafin daga baya ta soke sunansa.

INEC ta sanar cewa baturen zabenta da ya sanar da sunan Alhassan Doguwa a matsayin wanda ya yi nasara, ya yi haka ne domin kubutar da ransa.

Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai, ya bayyana cewa bambancin da ke tsakanin kuri’un ’yan takara biyu da ke kan gaba (APC da NNPP) bai kai ywan kuri’un da aka soke a rumfuna zaben 13 ba.

A cewarsa, mutum 6,917 ne suka karbi katin zabe a wuraren, kuma bambancin kuri’un da ke tsakanin wanda ya fi samun kuri’u da mai bi masa 4,934 ne.

Aminiya ta kawo rahoton yadda kotu ta tsare Doguwa a gidan yari, kan zargin harin da aka kai wa cibiyar tattara sakamakon zaben da kuma ofishin jam’iyyar adawa ta NNPP a Karamar Hukumar Tudun Wada.

Daga bisani kotun ta ba da belin sa a kan Naira miliyan 500, bayan ya shafe kwana shida a tsare.

Kotun ta kuma haramta masa zuwa mazabarsa a lokacin zaben gwamna da ’yan majalisar dokoki ta jiha da za a gudanar a ranar Asabar 11 ga watan Maris, 2023.