INEC za ta yi gwajin tantance masu zabe a watan Fabrairu
Muna neman hadin kan masu katinan zaben da rumfunansu suka fito a wadanda za a yi gwajin.
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanya 4 ga watan Fabrairu a matsayin ranar soma aikin gwada tantance masu kada kuri’a da ma’aikatanta a cibiyoyin zabe 436 na Najeriya.
Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan ranar Juma’a yayin taron da ya gudanar tare da jagororin hukumar.
Yakubu ya ce horon za a gudanar da shi ne a cibiyoyi 12 na jihohin kasar, da kuma guda hudu a Birnin Tarayya, Abuja.
“Kamar yadda kuka sani INEC za ta yi amfani da na’urar BVAS don tantance masu kada kuri’a a Babban Zaben Kasa.
“Haka ne ya sanya muka yi gwajinsu a ofisoshinmu don tabbatar da ingancin aikinsu.
“Mataki na gaba shi ne yin gwajin akan masu kada kuri’a da ma’aikatan da za su yi aikin.
“Saboda haka za mu yi gwajin kamar yadda muka yi gabanin zaben Gwamnan Jihar Osun da Ekiti na baya.
“Kuma za a fitar da cikakkun sunaye da lambobin rumfunan zaben da za a yi gwajin a shafin INEC na yanar gizo nan ba da jimawa ba,” in ji shi.
Yakubu ya roki masu katinan zaben da rumfunansu suka fito a wadanda za a yi gwajin, da su bai wa hukumar hadin kai su bayyana a ranar da aka tsara domin tantance su.