‘Inganta asibitoci ya kyautata harkar kiwon lafiya a Jihar Kano’

Babbar Jami’a mai kula da babban asibitin Dawakin Tofa da ke Jihar Kano Hajiya Fatima Abdullahi ta ce yadda ake kyautata yanayin asibitoci da sauran cibiyoyin shan magani a jihar ya taimaka sosai wajen inganta kula da lafiya a yankunan karkarar jihar.Hajiya Fatima Abdullahi ta bayyana haka ne a ganawarta da Aminiya, inda ta ce […]

‘Inganta asibitoci ya kyautata harkar kiwon lafiya a Jihar Kano’
‘Inganta asibitoci ya kyautata harkar kiwon lafiya a Jihar Kano’

Babbar Jami’a mai kula da babban asibitin Dawakin Tofa da ke Jihar Kano Hajiya Fatima Abdullahi ta ce yadda ake kyautata yanayin asibitoci da sauran cibiyoyin shan magani a jihar ya taimaka sosai wajen inganta kula da lafiya a yankunan karkarar jihar.
Hajiya Fatima Abdullahi ta bayyana haka ne a ganawarta da Aminiya, inda ta ce asibitocin jihar suna samun kulawa ta musamman daga gwamnati mai ci, sannan ana kokari kwarai wajen samar da kayan aiki ingantattu domin ci gaba da gudanar da aiki.
Hajiya Fatima ta ce ana samun nasarori wajen kula da marasa lafiya musamman ganin cewa gwamnatin jihar tana bai wa fannin kula da lafiya muhimmanci a koyaushe wanda hakan abin yabo.
Shugabar ta ce Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano a karkashin jagorancin Dokta Aminu Tsanyawa tana kokari wajen tsara tafiyar da aikace-aikacen kula da lafiya a dukkan shiyyoyin da ke jihar, kuma duk jami’an aikin jinya da masu kula da asibitoci suna kokarin tafiyar da aiki dare da rana ba tare da nuna gajiyawa ba.
Daga karshe, Hajiya Fatima ta yi godiya ta musamman ga Gwamnan Jihar Dokta Abdullahi Umar  Ganduje saboda ayyukan da gwamnatinsa ke yi a asibitin Dawakin Tofa da kuma karamar Hukumar Dawakin Tofa bisa kokarin da suke yi wajen kula da asibiti, kuma ta yaba wa daukacin ma’aikatan asibitn wadanda suke aiki ba tare da gajiyawa ba, inda ta yi kira ga jama’a su rika zuwa asibiti a duk lokacin da suka ji alamun rashin lafiya domin daukar mataki a kai.