Ingantaccen ingarman indararon Inda-sisi

Alif silin nunin kasan madambacin nunin kasa An kafa hukumar tushintasa Asusun dukiya ya san makamar masa ’Yan damfara kar sui kissa Ana bikin hawa kimar benen bisa   Hada-hadar lallaga sisi A Haurubja Ko Jihar Logar-sisi Hukuma ta bayar da lasisi Asusun da bakarfanfanarasi Akwai shakku da wasi-wasi   Wasu sun sha zama Wasu […]

Ingantaccen ingarman indararon Inda-sisi

Alif silin nunin kasan madambacin nunin kasa

An kafa hukumar tushintasa

Asusun dukiya ya san makamar masa

’Yan damfara kar sui kissa

Ana bikin hawa kimar benen bisa

 

Hada-hadar lallaga sisi

A Haurubja Ko Jihar Logar-sisi

Hukuma ta bayar da lasisi

Asusun da bakarfanfanarasi

Akwai shakku da wasi-wasi

 

Wasu sun sha zama

Wasu na lasar maskin madin zuma

Wa-ka-ci-ka-tashin ’yan zalama

Wadanda suka tumurmushe al’umma

Wafciyar sukuwar ingarma

 

Ja-gaban wannan lamari

Shi ne Umari

Da ya jajirce kan aiki nagari

Kariyar asusun ajiyar mutan gari

Muna nai maka barka da kokari

 

Ka  san akwai sasari

Miyagu sai an sa su  mari

Kumatunsu na ta kumburi

Sun washe mai tumaturi

Masu kayan miya a dai yi jimiri

 

 

Inda-indarin dararo

In’inar karo-karo

Turnukun tasgaro

Gurmuzun gwagwiyar goriyar goro

Kugin kankareren karo

 

Dabarbarun dunguren duguro

In yidirar dirkowar daro

Kwararar kudi kwararo-kwararo

Wasu daure da kyauro

Sun warwatse sun zazzaro

 

Ruwan kudi

Rajinrurin kaudi

Ragargazar radadi

Rugumniyar rudi

Rarumar ridi

 

Shekaru kofar hancin zagaye

Asusu-asusun ajiye-ajiye

Ana ta kokari a kiyaye

Asara a tarairaye

Sha’anin shan-kan shakiyai yai kaye

 

Indai da sisi

Kwabo da taro ba wasi-wasi

’Yan kasuwa asin-da-asin asi

Daga birnin Dabo zuwa Kumasi

Hada-hadar dukiya ana bin bahasi

 

Ka da a nunke al’umma a baibai

Ana ta kwashe musu kwabbai

Turmin dakan dukiya ya haifar da tabbai

Motsin mutsuttsuke matsabbai

Mutane sun karke da jawabai

 

Asusun karfin giwa

Ajiya na wulkitawa

Mai dukiya na fantamawa

Ma’aikata na shakatawa

Rabon riba na dada hauhawa

 

Mabudin dutse

Fatara an kwamtse

Talalar talauci ta katse

Masu dandatsa ban da kutse

Hada-hada ake a kimtse

 

Asasin assasa as-as

Mai tulin kudi cunkus

Mai dukiya kan kari kan ji dumus

’Yan kwadago a lumanar lumus

Ba rade-raden gulmar kus-kus

 

An dai kiyaye asara

Da toshe kafar algarara

Aka kuma kara

Da daurin damara

Shige da ficen kudi ba jira

 

Burgamen bajintar Santali

Tarin dukiya tuli-tuli

Aiki ake da natson hankali

Ba a fatali

Ko kwasar kudi ai shagali

 

Uba mai tarairayar dukiyar  ’ya’ya

Asusun ka ya biya awalajar kaya

Masu dako sun san an biya

Matsabbai sun yi zirya

Hukumar Inda-sisina ta bibiya

 

Kakkarfan Ingarma

Gadon bayansa kudi sui magama

An dai hana karma-karma

Ko na kudin cizo da kuma

A dai kiyayi dama-dama

 

Dakon dakon dukiya

Dakin dakan dakakkiya

Daurin damarar dawainiya

Daure-dauren daddake dirkaniya

Dogewar doke danniya

 

Inda-sisi

Kar ai kwafsi

A kare taro da sisi

Kowa ya samu natson lasisi

Kar a zo ana laluben asi

 

Hukumar hada-hadar hantsewar hatsin hantsin hasafin kariyar asusu-asusun ajiyar al’umma a kasar Haurobiya ta yi bikin cikarta shekaru kofar hanci da zagaye da kafuwa, inda ake ta murna kan irin wannan kimar matsayi da ta kai. Wannan sha’anin biki ya wakana ne tare da gunduma-gunduman bakin da aka gayyato daga ciki da wajen kasar nan. Kusan kowa sai sambarka ya yi wa wannan  hukuma, musamman Malam Umari da ke jan ragamar babban al’amari, wajen kare matsabban mutanen gari, wanda aka yi masa barka da kokari, musamman yadda ya jajirce da kwazon aiki nagari.

Ni kuwa na fasko cewa, a wajen bayar da kariyar kange kasassabar assasa asarar asusu-asusun ajiye-ajiyen al’umma, wannan hukuma ta Inda-sisi mai bin bahasin tarin taro da sisi tana da jan aiki a gabanta, musamman in an yi la’akari da yadda a ’yan shekarun nan ’YAN DAMFARAR DAMUN-FURA, suka ci kolonsu babu babbaka, har ta kai ga an tsuwurwurta turka-turkar takun sakar TURMIN DAKAN HAURO da MOTSIN MUTSUTTSUKE MATSABBAI, inda Mai-burodi ya yi bidiri birede da dukiyar Haurobiyawa, inda daga bisani ya garkame gambu da jimamin jama’a. A daidai lokacin da Haurobiyawa ke fama da tataburzar tarnakin tafkar Mai-burodi, da aka koka wa Malam Umari, cewa ya yi, su dai a Hukumar Inda-sisi du’a’in rokon Mai-duka kawai za su yi wa al’umma, don tuni suka ja na-zomon al’umma kan lallai su kiyayi masu walwalin waliyon walankeluwar wulkice-wulkicen wulwulawar wa-ka-ci-ka-tashin  watayawar walwalar wala-wala. Kuma da barewa ta arce da damin matsabban al’umma a zamanin mulkin Baba-ojo mai gonakin Otawa, shin wane namijin yunkuri wannan hukuma ta tabuka don rage radadin asara?

Uwa-uba, wannan Hukuma ta Inda-sisina tana sane da cewa an antayo damin matsabban garkuwar gagara-kuwwa da matsabban damfarar damun-fura a asusu-asusun ajiyar da ke fadin Haurobiya, shin ko ba za ta iya bai wa ’yan kasa kariya ba ne?

Akwai azargagiyar zizarar ziryar zarge-zargen cewa, hadin bakunan ’yan kwadagon da ke laluben kadago a asusu-asusun ajiya na da hannu dumu-dumu wajen tafka ta’asa, shin ko Inda-sisi ta taba bin kadin lamarin?

Al’amuran dai da ke cutar da hada-hadar Hauro sanannu ne, don haka sai a kauce wa Inda-indar indararo ko dirar dirkowar darewar daro da kwararar da kudi a kwararo-kwararo, musamman wadanda ke daure a kyauro gudun kada su warwatse su zazzaro. Domin wadansu za su baza laftun labarai cewa, ana ta ruguntsumin ruwan kudi, tare da rajin rurin kaudi mai ratattakar rangajin ragargazar radadi a rugumniyar rudin rarumar ridi.

Kuma shekaru kofar hanci da zagaye na Hukumar Inda-sisi asusu-asusun ajiye-ajiye na ta kokarin kiyaye asara  a tattare, a  tarairaye- tarairaye wajen sha’anin shan-kan shakiyai gudun kaye. Shi ke nan in dai da sisi, kwabo da taro ba wasi-wasi  a  tsakanin ’yan kasuwa masu tarin asi, wato daga birnin Dabo zuwa kasar Ghana a yi gane-gane a birnin Kumasi, wajen hada-hadar dukiya ana ta bin bahasi.

Abin taradaddi dai, shi ne, kada a nunke al’umma a baibai, har a kwashe musu kwabbai, tamkar dai yadda lamura suka wakana a dakan turmin dakan dukiya, wanda ya haifar da tabbai, aka zo aka karke a motsin mutsuttsuke matsabbai, har mutane suka karke da janjanin jawabai

Lallai akwai bukatar bai wa Haurobiyawa tabbacin cewa akwai lullumin lumanar luntsumar lumui-lumui lumus a tsakanin wannan hukuma da asusu-asusun ajiyar al’umma da suka hada da: Katuwar giwa da kakkarfan ingarma da Uba da Burgamen bajintar Santali da Asasin assa as-as da makamantansu. A yi ta fafutikar yaye duhun juhala don tabbatar da adala, gudun kwamacala, ta yadda za a yi ta hada-hada bisa ka’idojin doka, kada kowa ya koka. A kiyayi kidahumanci, a yi komai cikin mutunci, tare da kauce wa camamar ci-mu-cin cincirindon cin ca’ammas ko cuku-cukun cacumar cukubus da artabun aikin amso alkubus.

A dai yi hattara, a kauce wa LAFTUN LISSAFIN LIYAFAR LAIFUFFUKAN LUKUDIN LAKUME-LAKUMEN LAMUNI. Domin irin wannan ta’asar ke haifar wa harkokin hada-hadar tattalin tulin tuttule tulu, ai ta kwan-gaba, kwan-baya. Karshe dai a yi ta jefa azargagiyar zarge-zarge a inda ba su dace ba, har hakikanin wadanda suka tafka ta’asa a kwanon tasa su samu sarari su arce, ba wani ka-ce-na-ce.

Mu dai ’yan makarantar Dodorido mahayan shorido, muna matukar kyarar INDA-INDAR IN’INAR INDARARON INDA-SISI, amma muna matukar kaunar INGANTACCEN INGARMAN INDARARON INDA-SISI. Domin ta haka ne kawai za a bi kadin batan dabon taro da sisi, tare da bin bahasi kan kowace karfamfanar assasa asarar asi.

Matukar makekiyar hukumar tarairayar takure turka-turkar asarar ajiyar asusu na son ta ci gaba da karin shekaru masu albarka, sai ta himmatu ka’in-da-na’in wajen tunkude tarnakin tataburzar turka-turkar tauye hada-hadar hambudar handamar hautsinin hantsewar hatsin Haurobiyawa. Kai kodai so ake a karke da kafa kwatankwacin Hukumar AMAN-KUNU, wadda ta cefano asarar kamfanoni da asusu-asusun ajiya da suka durkushe ko samarin-kusu da ’yan matan jaba da gafiya suka yi musu murkusun muku-mukun makurar karkaf, inda suka wawushe komai-da-komai, har ma suka bi da maimai, ba tare da wata manufa takamaimai ba, amma har yanzu ba ta halarto da irin dimbin nasarorin da ta samu wajen juya asara ta zama gagarumar gwaggwabar riba ba?

 

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos