Ingantaccen tsarin jarabawa ke jaddada mutunci da kimar kowace jami’a –Farfesa Akper

Farfesa Godwin Akper shi ne Daraktan Cibiyar Jarabawa da Tantancewa (DEA) na Budaddiyar Jami’a ta Najeriya (NOUN). A tattaunawarsa da JOEL NKANTA kwanakin baya a Uyo, Jihar Akwa Ibom, ya yi bayyani dalla-dalla dangane da abin da ya shafi harkar jarabawa ta keke-da-keke, da kuma dalilin da ya sanya aka daga batun jarabawa ta hanyar […]

Ingantaccen tsarin jarabawa ke jaddada mutunci da kimar kowace jami’a –Farfesa Akper

Farfesa Godwin Akper shi ne Daraktan Cibiyar Jarabawa da Tantancewa (DEA) na Budaddiyar Jami’a ta Najeriya (NOUN). A tattaunawarsa da JOEL NKANTA kwanakin baya a Uyo, Jihar Akwa Ibom, ya yi bayyani dalla-dalla dangane da abin da ya shafi harkar jarabawa ta keke-da-keke, da kuma dalilin da ya sanya aka daga batun jarabawa ta hanyar na’urar kwamfuta. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

 

A wannan karon, an fara jarabawa a kurace, ba kamar yadda aka saba ba, babu mamaki hakan ya faru ne saboda matsalar na’ura da aka samu a turakar jami’ar a farkon shekarar nan. Me za ka ce game da jarabawar keke-da-keke da aka kammala kwanan nan?

A takaice zan iya cewa mun samu maki 85 cikin dari. An samu nasara kwarai da gaske, duk da cewa mun dan samu ’yar matasala nan da can, wadda ba ta wuce kashi 15 cikin dari ba. Amma duk da haka za mu iya cewa mun samu gamsassar nasara.

 

Mafi yawan daliban da suka rubuta jarabawar, sun koka da cewa akwai matakan tsaro masu tsauri a wannan karon, idan aka kwatanta da tsarin jarabawar baya. Ko mene dalilin daukar wannan mataki na tsaro a wannan karon?

Ana auna mutunci da kimar kowace jami’a ne ta la’akari da yadda take tsara jarabawarta da yadda take auna dalibai. Bisa la’akari da ka’idojin jarabawarmu, shi ya sa muka tankade muka gyara tsarin, domin fitar da duk wata kafa da za ta yi wa tsarin namu kafar angulu. Mun samu nasarar daukar matakan da suka dace a dukkan wuraren da muke ganin za mu samu cikas, musamman ta abin da ya shafi kudi, zirga-zirga da sauransu kuma daidai gwargwado mun samu nasarar aiwatar da komai bisa dacewa.

 

Ko me ya sanya aka soke tsarin jarabawa ta intanet?

To za mu iya cewa akwai al’amura da dama da suka sanya aka dauki wannan mataki. Wasu daga cikin dalilan sun hada da na batun kudi da kuma na zirga-zirga. Haka kuma akwai batun bin tsare-tsare da ka’idojin jarabawa, inda muka lura da cewa akwai inda aka kauce ka’ida, wanda haka ya sanya aka dakatar da tsarin, har sai an daidaita al’amura sannan sai a dawo da tsarin.

 

Shin ko an samu satar fitar tambayoyin jarabawar da farko? Ana yada jita-jitar cewa abin day a faru ke nan, yaya abin yake ne?

Abin da ya kamata mu fahimta shi ne, akwai wasu tsare-tsaren jami’a, inda akwai bayannan da Shugaban Jami’a ne kadai ko Magatakarda zai iya fitar da su, don haka ni ba zan ce komai ba a kan wannan.

 

Ko za a iya cewa kowace matsala ma aka samu, ko sun faru ne bisa sakacin wasu jami’ai daga jami’ar, wato bara-gurbi?

Al’amarin nan dai ana kan bincikensa, don haka bai kamata in bayyana abin da ake kai ba, alhali ba a karkare bincike ba. Amma akwai bayanin da ke cewa an yi mana kutse a rumbunmu na adana bayanai. Domin sanin yadda haka ta faru, dole sai dai kwararru ne za su iya tantancewa. Mu dai a nan, mun kammala rahotonmu kuma mun mika shi ga inda ya dace, ana duba shi. Kuma nan gaba za a yi ta gudanar da taruka a makon nan. A sakamakon taron nan, za mu iya sani wasu abubuwan da suka faru domin daukar mataki domin gaba, sannan sai a tunkari batun jarabawa ta na’ura, kamar yadda ake yi a baya.

 

Tun da farko, cibiyarku ba ta yi wani shiri ba, yadda kamar yadda aka samu wannan matsala sai a karkata zuwa wani shiri na biyu, wanda kawai sai a aiwatar da shi, maimakon soke wannan tsari na jarabawa ta hanyar na’ura?

Ya kamata ka fahimci cewa, hanyoyin da muke bi muna gudanar da jarabawarmu ta hanyar na’ura ta bambanta da yadda wasu suke yi. Akan samu tambayoyi ne daga malaman da suke koyar da kwasa-kwasan, wadanda ke kai su zuwa tsangayarsu, sannan su shiga kai tsaye zuwa rumbun adana bayananmu, wanda cibiyoyin MIS da DEA ke kula da shi. An samu wasu mushkiloli, don haka sai muka mika batun ga cibiyoyin MIS da DIC. Su ne ke kula da dukkan al’amuran da suka shafi hikimomi da tsare-tsaren jarabawa ta hanyar na’ura, wato turakar intanet ke nan. Abin da ya faru shi ne, Cibiyar DEA sai ta aika jami’anta suka yo kwas na sani makamar aiki, wadanda ke kula da shiyyoyi 12 na kasar nan. Ta haka ne suka san abin da duk ake bukata domin gudanar da wannan turaka daga sassa daban-daban na kasar nan. Lokacin da suka tattara wadannan bayanai, sai aka samu matsala, yadda daga can sassan, suka kasa tuntubar babbar turakar jami’ar. Mu dai mun dogara ne ga wadannan jami’ar, su kuma sun nuna cewa akwai matsala kuma ana bukatar kudin da za a sawo manyan na’urorin da za su iya daukar wadannan manhajoji masu girma. An yi rashin dace hukumar jami’a ba ta amincec da batun kudaden sayo kayan ba, ga shi kuma lokacin jarabawa ya kure, don haka ya zama dole a dauki wannan mataki da aka dauka dangane da jarabawa. 

 

Me ya sanya cibiyoyin DEA, MIS da DICT suka ki daukar kiran waya daga daraktoci bayan da aka soke tsarin jarabawa ta hanyar na’ura?

A’a, haka ba ta faru ba. A lokacin da na nemi bukatar a soke jarabawa ta hanyar na’ura, ina rangadin duba yadda ake gyaran jarabawa a Inugu. A kan hanyata ta zuwa Inugu, ina duba cibiyoyi da yadda suke tafiyar da al’amuransu da wannan na’ura, domin mun fara ne kuma an yi ta samun matsaloli. Ba zan zauna a ofis kawai a Abuja ba, kuma in yi tsammanin zan samu bayanai da suka dace ba. Don haka sai na fara daga Abuja, na je Wuse II na je Lafiya. Daga Lafiya na nufi Makurdi zuwa Otukpor. Daga Otukpor na nufi Inugu. Ta hanyar wadannan tafiye-tafiyen ne na gano cewa ga matsalolin da ake fuskanta kuma na ci gaba da magana da jami’anmu na sassa daban-daban. Ta haka suka rika bin kadin mnatsalolin suna daukar matakan da suka dace, ni kuma ina ba su shawarwarin abin da ya dace. Lokacin da na isa Inugu, na ci gaba da magana da sauran sassa da ke fadin kasar nan, domin ganin yadda za a shawo kan dukkan matsalolin. A lokacin da na ankara da cewa babu yadda za a yi a magance matsalolin nan kuma a ce za a gudanar da tsarin jarabawar ta na’ura, sai na nemi izinin shugaban gudanarwar jami’a, cewa ya kamata a soke batun tsarin jarabawar ta na’ura a wannan karon har sai nan gaba. Ba zan iya dakatar da tsarin sannan in ci gaba da zama a Inugu ba, dole ne in tafi Abuja, mu shirya taro domin ganin yadda za a bullo wa al’amarin. Dalili ke nan na yi ta zirga-zirga, wasu wuraren ma nakan iske babu netwok, amma inda babu matsalar netwok nakan yi magana da mutane kuma a samu gamsassun bayanai. Na yi magana da Lafiya da Sibil Difens da Jalingo da Asaba da Bauchi da Kaduna. Haka kuma na yi magana da Farfesa Joktan. Duk wadannan, na yi magana da su a lokacin da nake kan hanya. Na yi magana da shugabanni tsangayoyi daban-daban, musamman shugabar tsangayar Kimiyyar Lafiya, tana nan, za ka iya tambayarta yadda muka yi.

 

Ko kana da wani sako ga ma’aikata da dalibai dangane da wannan kalubale da ake fuskanta yanzu?

Wannan al’amari dai na tsarin gudanarwa ne, shi kuma tsari ci gaba yake da gudana yau da kullum, ba za a iya cewa an samu kwarewa a kan tsari kaza ba cikin lokaci guda. kasar Romaniya, ba rana guda aka gina ta ba. Don haka muna ba da hakuri bisa ga matsalolin da aka fuskanta. Irin radadin da aka samu, da lokacin da aka bata da kuma asarar kudaden da aka yi a sakamakon haka, duk muna ba da hakuri. Ni ne shugaban cibiyar DEA, don haka mun dauki alhakin duk mushkilar da ta faru, don haka muna ba da hakuri ga kowa da al’amarin nan ya shafa.