Ingila ta fadada tallafinta ga Najeriya da Fam miliyan 200
A ranar Larabar makon jiya ce, Sakatariyar Hukumar Bunkasa kasashe ta Ingila, Priti Patel ta bayyana fadada tallafinta ga Najeriya da Fam miliyan 200 da za ta bayar cikin shekara biyar, domin kare mutum miliyan daya da rabi daga fadawa cikin fari da kuma yadda zai tallafa wajen ajiye yara maza da mata dubu 100, […]

A ranar Larabar makon jiya ce, Sakatariyar Hukumar Bunkasa kasashe ta Ingila, Priti Patel ta bayyana fadada tallafinta ga Najeriya da Fam miliyan 200 da za ta bayar cikin shekara biyar, domin kare mutum miliyan daya da rabi daga fadawa cikin fari da kuma yadda zai tallafa wajen ajiye yara maza da mata dubu 100, don su ci gaba da karatu a makarantunsu. Haka tallafin ya hada da abin da ya danganci dawo da zaman lafiya a Arewa maso Gabas. Ta bayyana haka ne a yayin da ita da Sakataren Harkokin kasashen Waje na Ingila, Boris Johnson suka kai ziyara zuwa Maiduguri, Jihar Borno. Wannan shi ne karo na farko da manyan jami’an suka fara fita tare, kuma sun yi haka ne domin su jajanta wa Najeriya da karfafa mata gwiwa, wajen yakin da take yi da ’yan ta’adda. Johnson ya ce yana alfahari da tallafin da Ingila ta bayar: “Wannan wani yunkuri ne na tallafa wa abokiyar hulda a lokacin da take bukata, wanda zai magance kalubalen da ke addabar duniya ta ’yan gudun hijira.”
A yayin ziyarar, sun gana da mutanen da suka tsira daga ta’addancin Boko Haram da wadanda suka samu raunuka a sanadiyyar tashin bama-bamai ko harbin bindiga. Haka sun gana da mutanen da suka rasa matsugunnansu. Patel ta bayyana wannan ta’addanci da abin takaici, inda ta ce mafi yawan yaran da abin ya shafa suna fuskantar ukubar yunwa a matakai daban-daban. Wannan karin tallafi da kasar ta Ingila ta bayyana, kari ne kan wanda ta dade tana bayarwa, tallafin da ya hada da horar da sojojin Najeriya dubu 28 da kuma girke sojojin Ingila sama da 40, domin taimaka wa dakarun Najeriya.