Ingila ta yi waje da Najeriya a Gasar Kofin Duniya ta Mata

Ingila ta karasa wannan wasa da ‘yan wasa 10 har zuwa matakin karin lokaci.

Ingila ta yi waje da Najeriya a Gasar Kofin Duniya ta Mata

Tawagar kwallon kafar mata ta Ingila ta yi waje da ta Najeriya a matakin sili daya kwale na Gasar Kofin Duniya ta 2023 da ke gudana a New Zealand da Australia.

Tawagar Three Lionesses ta fatattako Super Falcons ne bayan da ta doke ta ci 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron raga a yau Litinin.

Wannan ya biyo bayan canjaras ne wanda babu ci da bangarori biyun suka yi a wannan safiya ta Litinin, a wasan da ya bai wa masoya kwallon kafa nishadi.

Ingila ta karasa wannan wasa da ‘yan wasa 10 har zuwa matakin karin lokaci, bayan da a minti na 87 alkaliyar wasa ta sallami Lauren James, shahararriyar ‘yar wasansu, wadda ta ci kwallaye 3 a matakin rukuni.

Cikin fushi Lauren ta taka bayan Michelle Alozie wadda ta fadi kasa a minti na 87, bayan kwallo ta kubuce daga kafarta.

Ingila za ta yi karon batta da Jamaica ko kuma Colombia a wasan daf da na kusa da karshe a birnin Sydney, ranar Lahadi.