Injiniyan Najeriya ya kera motar da za ta iya tashi sama a Borno

Ya kera motar ce a Maiduguri

Injiniyan Najeriya ya kera motar da za ta iya tashi sama a Borno

Wani fasihin injiniya a Jihar Borno, Abba Dalori, ya kera tare da hada wata mota da za ta iya tashi sama a jihar.

Abba dai ya kammala karatun digirinsa a Jami’ar Maiduguri, inda ya samu digiri a bangaren Injiniyanci.

Injiniya Dalori ya kwashe shekaru yana kera motar da za ta tashi da kuma tuki a kan hanya kamar yadda ya bayyana.

A cewarsa wannan kirkirar tasa ya yi amfani  ne da wasu abubuwa ma su kamar farfela guda biyu masu karfi ya sa a sama da bayan motar don taimaka mata ta samu ta tashi daga kasa zuwa sama.

Dalori ya ce yana fatan motarsa da ke iya tashi za ta zaburar da sauran matasan Najeriya don ba su kwarin gwiwar ci gaba da sha’awarsu da samar da sabbin hanyoyin ciyar da kasar su gaba wajen kere-kere.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos