Inshorar lafiya: An kaddamar da sabon tsari domin iyalai

GIFSHIP sabon tsari ne na inshorar lafiyar iyalai da daidaikun jama’a

Inshorar lafiya: An kaddamar da sabon tsari domin iyalai

Gwamnatin Tarayya ta bullo da sabon Shirin Inshorar Lafiyar Iyalai (GIFSHIP) da zummar ba dukkannin iyalai a Najeriya damar cin gajiyar tsarin inshorar lafiya.

Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, yayin kaddamar da GIFSHIP a ranar Alhamsi ya ce  shirin ya samu ne sakamakon darussan da aka koya a lokacin aiwatar da magabacinsa na VCSHIP wanda ake hadada a ciki.

Ehanire ya ce sabon shirin zai magance kalubale da matsalolin da hukumomi da masu cin gajiya suka fuskanta a lokacin aiwatar da VSCHIP, wanda tsari ne na adashin gata.

A cewar ministan, baya ga kawar da matsalolin da aka fusktan a bayya, sabon shirin inshorar lafiyar zai inganta tsari tare da fadada VCSHIP ta yadda karin jama’a za su amfana su kuma samu biyan bukata.

Babbar manufar GIFSHIP, a cewarsa, ita ce fadada tsarin kula da lafiya ga dukkannin ’yan kasa a Najeriya.

Da yake bayani, Babban Sakataren Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIS), Farsesa, Sambo Muhammad, ya ce sabon tsarin na GIFSHIP zai ba wa iyalai da daidaikun mutane damar cin gajiyar inshorar lafiya.