Inuwa Yahaya ba zai iya kayar da dankwambo ba – A. A. Abubakar
Wani matashin dan siyasa a Jihar Gombe kuma dan Jam’iyyar APC Ahmad Adamu Abubakar, ya ce dan takarar Gwamna na jam’iyyarsu ta APC Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, ba zai iya kayar da Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo a zaben ban aba. Ahmad Adamu Abubakar, ya ce abin da ya say a fadi haka ne shi ne […]
Wani matashin dan siyasa a Jihar Gombe kuma dan Jam’iyyar APC Ahmad Adamu Abubakar, ya ce dan takarar Gwamna na jam’iyyarsu ta APC Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, ba zai iya kayar da Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo a zaben ban aba.
Ahmad Adamu Abubakar, ya ce abin da ya say a fadi haka ne shi ne jam’iyyarsu ta APC ta fitar da dan takarar da bai cancanta ba, kuma bai da magoya baya.
“Ni mutum nake yi ba jam’iyya ba shi, ya sa ina APC, amma ba zan zabi dan takarar da aka tsayar mana ba, saboda ba zai iya cin zabe ba, kama-karya Sanata danjuma Goje ya yi ya sa ya ci zaben fidda-gwani. Tun a lokacin mu ’yan Jam’iyyar APC muke ganin cin zabensa zai yi wuya,” inji shi.