Inuwar Sunnah ta yaba wa Ganduje kan karfafa zaman lumana a tsakanin addinai

Wata kungiyar hada kan al’umma a kan tafarkin sunnah a Najeriya, ta bayyana farin cikinta da goyon baya ga Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje a kan kokarinsa na hada kan mabiya addinai a Jihar Kano.kungiyar ta ce hakan ya kyautata fahimtar juna da karfafa zaman lumana a tsakanin mabiya addinan, musamman a wannan […]

Inuwar Sunnah ta yaba wa Ganduje kan karfafa zaman lumana a tsakanin addinai
Inuwar Sunnah ta yaba wa Ganduje kan karfafa zaman lumana a tsakanin addinai

Wata kungiyar hada kan al’umma a kan tafarkin sunnah a Najeriya, ta bayyana farin cikinta da goyon baya ga Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje a kan kokarinsa na hada kan mabiya addinai a Jihar Kano.
kungiyar ta ce hakan ya kyautata fahimtar juna da karfafa zaman lumana a tsakanin mabiya addinan, musamman a wannan lokaci da ake kokarin kawo karshen matsalar ta’addanci a kasar nan.
Shugaban kungiyar Malam Ali dan Abba ya bayyana haka a yayin zantawa da wakilinmu a Abuja.
Malam Ali dan Abba wanda shi ne Shugaban Kwamitin Watsa Labarai na kasa na kungiyar Izala, ya ce abin da Gwamnan ke yi zai kawo karin yarda da zaman amana a tsakanin kungiyoyin mabiya addinai da suka kunshi na Musulmi da na Kirista sannan ya kawar da zaman gaba.
Shugaban kungiyar Inuwar Sunnah ya ce Allah Ya hada al’ummar Najeriya mabambantan juna a kasa guda, saboda haka wajibi ne jama’a su rika yi wa juna uzuri da mutunta hakkin kowa.
Ya ce ya ki da matsalar satar shanu da Gwamna Ganduje ya yunkuro a kai ta dakile barnar a yanzu, saboda haka ya yi kira ga jama’ar jihar su ci gaba da bai wa Gwamnan goyon baya don samun nasara a sauran ayyukan ci gaba da ya sa a gaba.