Inyamuri da kudi
Inyamuri da kudi Wani Inyamuri ne ya yi hadari da sabuwar motarsa mai tsada, ya yi kokari ya tashi ya kira dan sanda ta waya. Da ya iso wurin sai ya ce masa: “Don Allah ka duba ka gani, wannan mai motar ne kawai ya zo ya buga wa sabuwar motata mai tsada, ga shi […]
Inyamuri da kudi
Wani Inyamuri ne ya yi hadari da sabuwar motarsa mai tsada, ya yi kokari ya tashi ya kira dan sanda ta waya. Da ya iso wurin sai ya ce masa: “Don Allah ka duba ka gani, wannan mai motar ne kawai ya zo ya buga wa sabuwar motata mai tsada, ga shi duk ta lalace.” dan sanda ya girgiza kansa, ya ce wa Inyamuri: “Kai wane irin mutum ne, ta mota kake alhali ba ka lura ba cewa an datse maka hannu, ga shi nan yana ta zubar jini?” Inyamurin nan ya duba ya ga babu hannunsa daya, sai ya saka kuka, ya ce: “Chineke, ina agogona da zobbana na zinare!?”
Daga Bashir Yahuza Malumfashi, 08098157899
Kallon kwallo
Wata rana wani Bafillatani yana kallon kwallo, ya ga ana wasa a fili, ana fasin-fasin. A karshe ya ga duk gudun da suke yi sai ya ga gola yana rikewa kuma ya sake jefawa, sun bi da gudu. Sai ya tambayi na kusa da shi cewa: “Malam, wannan wadanne irin sakarkaru ne, suna ta gudu sun kasa kama kwallon amma wancen yana tsaye shi kadai ya kama kuma ya sake jefawa, yana hada su fada. Shin ba su da wayo ne?”
Daga Jibril Haruna Tela Lemu Zariya, 08063400251
Allah maimaita
Wani mahaukaci ne an yi rasuwa wani gida, sai ya zo ya zauna cikin masu karbar gaisuwa. Da aka kawo abinci sai aka zuba masa ya ci ya koshi. Da ya tashi tafiya, budar bakinsa ke da wuya sai ya ce: “Allah Ya maimaita.”
Daga Bashir Abdullahi Funtuwa, 08064677073
Bahaushe mai wayo
Wani Bafullace ne ya ji ’yan uwansa suna ta kuranta cewa Bahaushe yana da wayo, hikima da dabarun rayuwa. Ran nan sai shiga gari, ya hadu da wani mutum ya ce masa: “Na ji cewa Bahaushe mayen sani ne, to idan ka cika mayen sani, mene ne a aljihuna? Idan ka gane zan saya mana abinci da shi. Mutumin ya ce masa kudi ne. Bafulatani ya je ya sayo abinci, ya zo da kwanon a rufe ya ce masa: “Mene ne a nan ciki? Idan ka gane zan bude mu ci tare. Shi kuwa sai ya amsa masa da cewa abinci ne. Bafulatani ya ce: “Lallai Bahaushe mayen sani ne, to mu ci.”
Daga Abdullahi Musa Hadeja, 07066180429