IPOB: Gwamnonin Arewa sun yi tir da kisan Gulak

Kungiyar ta yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa Ahmed Gulak a Imo.

IPOB: Gwamnonin Arewa sun yi tir da kisan Gulak

Kungiyar Gwamnonin Arewa

Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF), ta bayyana kisan tsohon Mashawarci na Musamman ga Shugaban Kasa Goodluck Jonathan kan Harkokin Siyasa, Ahmed Gulak, a matsayin abin takaici mafi girma kuma abin Allah wadai.

A martaninsa game da kisan, Shugaban Kungiyar kuma Gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya ce abin bakin ciki ne kuma abun kyama.

“Mummunan abu ne wanda dole a yi tir da shi gaba daya,” inji shi.

Lalong ya ce dole ne a kalli kisan Gulak a matsayin laifi mafi muni, sannan ya yi gargadi cewa siyasantar da lamarin ka iya haifar da mummunan tashin hankali a kasa.

Ya ce rahoton da ’yan sanda suka bayar na ganowa da kuma kashe wadanda ake zargi da kisan marigayin dan siyasar, abun a yaba ne.

Shugaban kungiyar gwamnonin ya bukaci jama’a da su rika karfafa wa jami’an tsaro gwiwa don samun damar dakile ayyukan ta’addanci a Najeriya baki daya.

Ahmed Gulak ya gamu da ajalinsa ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama a Jihar Imo, inda ’yan bindiga da ake zargin ’yan haramtacciyar kungiyar IPOB ne suka harbe shi har lahira, da safiyar ranar Lahadi.