IPOB: Mahara sun kashe sojoji 5 da farar hula 1 a Anambra
Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’ya’yan haramtacciyar kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra (IPOB) ne, sun hallaka sojoji biyar da farin hula daya a Karamar Hukumar Orumba ta Kudu da ke jihar Anambra. Wani ganau ya ce da karfe 1:00 na rana zuwa 2:00 sojojin suka iso wurin a mota kirar Toyota Sienna domin […]
Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’ya’yan haramtacciyar kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra (IPOB) ne, sun hallaka sojoji biyar da farin hula daya a Karamar Hukumar Orumba ta Kudu da ke jihar Anambra.
Wani ganau ya ce da karfe 1:00 na rana zuwa 2:00 sojojin suka iso wurin a mota kirar Toyota Sienna domin sintiri, sai kawai maharan suka far musu.
- HOTUNA: Bikin karrama Jakadiyar Birtaniya a Najeriya
- An sanya dokar takaita zirga-zirga ta sa’a 24 a Edo
Sai dai kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, Ikenga Tochukwu, ya ce, “Ba zan iya tabbatarwa ko an kashe sojoji ba, amma na sa an samu harbe-habe a titin Umunze da ke daura da wani banki,” in ji shi.
Ikenga ya ce tuni rundunar ta tura jami’anta yankin, domin daidaita al’amura.
A baya-bayan nan dai ana ta samun kashe-kashe a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, wanda ake alakantawa da IPOB din, duk da ta sha musanta zargin.