Iraki ta kori Jakadan Sweden saboda kona Al-Qur’ani

Wani matashi Salwan Momika ne ya jagoranci kona Al-Qur’anin a Babban Masallacin Stockholm.

Iraki ta kori Jakadan Sweden saboda kona Al-Qur’ani

Iraki ta kori jakadan Sweden jim kadan bayan da masu zanga-zangar suka mamaye ofishin jakadancinta da ke Bagadaza tare da cinnawa wasu sassan ginin wuta.

Magoya bayan jagoran mazhabar shi’a na Iraqi Muqtada al-Sadr sun yi kira da a kona ofishin jakadancin Sweden din a ranar Alhamis.

Masu zanga-zangar dai sun fusata ne kan abin da ya ce shi ne karo na biyu da aka kona Qur’ani a gaban Ofishin Jakadancin Iraki da ke Stockholm.

A yayin da masu zanga-zanga a kasar Sweden suka yi ta harbi da kuma lalata wani littafi da suka ce Qur’ani ne, sai dai ba su kona shi ba kamar yadda suka yi barazanar yi.

Rahotanni na cewa, Salwan Momika dan gudun hijira dan kasar Iraqi mai shekaru 37 a kasar Sweden ne ya shirya lamarin wanda kuma ya kona shafukan Qur’ani a gaban Babban Masallacin birnin Stockholm a ranar 28 ga watan Yuni a lokacin bukukuwan sallah babba.

Lamarin da ya faru a watan da ya gabata ya fusata al’ummar Iraki da magoya bayan al-Sadr, wanda ke matsayin mai ra’ayin kishin jama’a, wanda a baya magoya bayansa suka mamaye majalisar dokokin Iraki, suka mamaye Ofishin Jakadancin Sweden a Bagadaza.

Wannan aika-aika ta haifar da zanga-zanga da dama a kasashen musulmi kamar yadda gwamnatoci a Iraki, Turkiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Jordan da Morocco suka yi tir da lamarin.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja