Iraki za ta amince a aurar da ’yan matan da shekarunsu suka kama daga 8 zuwa 9

Yanzu haka majalisar dokolkin Iraki ta fara yunkurin yin dokar da za ta amince wa mazaje aurar matan da shekarunsu suka kama daga takwas zuwa tara ba tare da matsala ba.  Haka kuma dokar za ta amince da mazajen su sadu da matan a duk lokacin da suke bukata ba tare da matan sun yi […]

Iraki za ta amince a aurar da ’yan matan da shekarunsu suka kama daga 8 zuwa 9

Yanzu haka majalisar dokolkin Iraki ta fara yunkurin yin dokar da za ta amince wa mazaje aurar matan da shekarunsu suka kama daga takwas zuwa tara ba tare da matsala ba.  Haka kuma dokar za ta amince da mazajen su sadu da matan a duk lokacin da suke bukata ba tare da matan sun yi musu gardama ba.
Kodayake dokar ba ta kayyade karancin shekarun da yakamata mace ta yi aure ba amma ta  yanke adadin shekarun da za a iya sakin mace idan ta kai su.  
A kasar Iraki, an kayyade sai yarinya ta kai shekara tara ne za a iya sakinta bayan an aureta. Dokar ta ce ana kyautata zaton idan yarinya ta kai shekara tara a lokacin ta mallaki hankalinta don haka babu laifi idan an sake ta a wannan lokaci.
Haka kuma dokar za ta haramta wa mata fita daga gidajen mazajensu ba tare da izini ba kuma za ta rage musu karfin ikon mallakar ’ya’ya idan an samu rabuwa a tsakanin miji da mata.
Sannan dokar za ta ba maza damar yin aure fiye da daya a duk lokacin da suka bukaci hakan.
Wata kididdiga da aka gudana a Iraki a shekarar 2011 ta nuna an samu kashi 25 daga cikin 100 na matan da aka yi musu aure ’yan kasa da shekara 10.
Kafar sadarwar  Associate Press (AP) ta ce a wani bincike na jin ra’ayin ’yan kasar da ta gudanar game da wannan batu da majalisar dokokin kasar ke yunkurin aiwatarwa da yawa daga cikin mutanen kasar musamman mata sun nuna rashin amincewarsu a kan haka.  Sun ce yin haka tamkar danne wa mata kasar hakki ne a cigaba da musgunawar da ake musu.