Iran da Amurka sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta

Hakan na zuwa ne bayan Amurka ta amince da wasu ƙa’idoji 10 da Iran ta gindaya a matsayin sharaɗinta

Iran da Amurka sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta

Gwamnatin Iran ta bayyana amincewarta da yarjejeniyar tsagaita wuta na makonni biyu a yayin da ake sa ran fara tattaunawar sulhu ranar Juma’a a ƙasar Pakistan.

Iran ta kuma sanar da amincewar ta buɗe Mashigar Hormuz gaba ɗaya ne bayan da Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya sanar da dakatar da kai mata hare-hare na tsawon makonni biyu.

Hakan na zuwa ne bayan Amurka ta amince da wasu ƙa’idoji 10 da Iran ta gindaya a matsayin sharaɗinta na amince da yarjejeniyar sulhu.

Hukumomin Iran sun bayyana matakin da aka kai a matsayin nasara ga ƙasar, inda suka bayyana cewa sun yi wa al’ummar ƙasar cewa za a ƙulla yarjejeniya ne bisa la’akari da ƙa’idodjin da ƙasar ta shimfiɗa.