Iran da Amurka sun daidaita tattaunawar sulhu a Switzerland
Sun bayyana cewa Iran da Amurka sun amince da kafa layin sadarwa don tabbatar da buɗe Mashigin Hormuz da kuma kawo ƙarshen faɗa a Lebanon a doguwar tattaunawar da ta ƙare a ranar Litinin.
Daga hagu: wakilin musamman na Amurka Steve Witkoff, Firai Ministan Pakistan Shehbaz Sharif, Mataimakin Shugaban Amurka JD Vance, da Shugaban Rundunar Sojin Pakistan Asim Munir, sun yi ganawa kafin a fara tattaunawa a Switzerland. [AFP]
Masu shiga tsakani sun bayyana cewa Iran da Amurka sun amince da wani tsari da zai kai ga yarjejeniya ta ƙarshe domin kawo ƙarshen yaƙin da ya ɗauki fiye da kwanaki 100.
Sun bayyana cewa Iran da Amurka sun amince da kafa layin sadarwa don tabbatar da buɗe Mashigin Hormuz da kuma kawo ƙarshen faɗa a Lebanon a doguwar tattaunawar da ta ƙare a ranar Litinin.
Sun sanar da haka ne bayan kammala zagayen farko na tattaunawa tsakanin manyan jami’an kasashen biyu da aka fara gudanarwa daga ranar Lahadi a kasar Switzerland.
Bangarorin, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Amurka JD Vance da Shugaban Majalisar Iran Mohammad Bagher Ghalibaf, sun fara tattaunawa ne bisa tsarin wata yarjejeniya ta wucin gadi da aka cimma makon da ya gabata.
- Kotu ta daure wata mata shekara 2 kan safarar jarirai
- Fira Ministan Birtaniya ya yi murabus
- An kona matar aure da ranta kan zargin satar yara a Kaduna
Masu shiga tsakani daga Pakistan da Qatar sun ce an cimma matsaya kan “taswirar da za kai ga yarjejeniya ta ƙarshe cikin kwanaki 60,” tare da ci gaba da tattaunawar fasaha a makon nan a Switzerland.
Sun ce, “An samu ci gaba mai ƙarfafa gwiwa, ciki har da ƙirƙirar tsarin tattaunawa na fasaha,” tare da kafa tashar sadarwa don kauce wa rikice-rikice da rashin fahimta game da Mashigin Hormuz.
Haka kuma, an amince da kafa wani “cibiyar kauce wa samun rikici” tsakanin ɓangarorin biyu da hukumomin Lebanon domin hana sake barkewar faɗa a can.
Aljazeera ta ruwaito cewa masu shiga tsakani sun yaba da yadda tattaunawar ta kasance mai ma’ana, tare da ƙara cewa tawagar aiki da aka kafa za su fara aiki nan da nan.
Sai dai ta ƙara da cewa, “Har yanzu akwai aiki mai yawa da ya rage, kuma ba a bayyana yadda za a tsara tawagar ba, ko irin rawar da za su taka, ko kuma tsarin tarurruka na gaba.”
A zahiri, Tehran ta toshe Mashigin Hormuz a matsayin martani ga hare-haren haɗin gwiwa da Isra’ila da Amurka suka kai a ranar 28 ga Fabrairu wanda ya tayar da wannan yaƙi.
Lebanon ta tsunduma cikin rikicin ne bayan Hezbollah mai goyon bayan Iran ta kai hari kan Isra’ila a matsayin martani ga hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran. Wannan ya sa Isra’ila ta kaddamar da harin boma-bomai da mamayar ƙasa a kudancin Lebanon.
Bayan jerin yunƙurin da bai yi nasara ba, Washington da Tehran a makon da ya gabata suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta fahimtar juna da nufin kawo ƙarshen yaƙin. Yarjejeniyar ta haɗa da tanadi na kawo ƙarshen faɗa tsakanin Isra’ila da Hezbollah a Lebanon.
Sai dai duk da haka, an ci gaba da samun hare-haren Isra’ila a Lebanon, lamarin da ya sa Iran ta bayyana cewa, bayan ta sake buɗe Mashigin Hormuz, za ta sake rufewa.
Wannan mashigi ne ake bi da kusan kashi ɗaya bisa biyar na man fetur da iskar gas na duniya kafin barkewar yaƙin.