Iran da Isra’ila: Saudiyya ta gana da shugaban Iran

Iran ta gargaɗi ƙasashen Larabawa cewa duk wadda ta haɗa baki da Isra’ila za ta yaba wa aya zaƙi

Iran da Isra’ila: Saudiyya ta gana da shugaban Iran

 

Shugaban Kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi wata ganawa da Ministan Harkokin Wajen Saudiyya, Faisal bin Farhan, kan rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.

Ganawar tasu a birnin Doha na ƙasar Qatar na zuwa ne a yayin da Iran ta ɗora ɗamarar yaƙi da Isra’ila da kuma kashedi ga ƙasashe Larabawa kan taimakon ƙasar Yahudawan.

Iran ta yi uwa ta yi makarɓiya ne bayan hare-haren Isra’ila da suka hallaka mutane da dama ciki har da shugabannin kungiyar Hisbullah da Iran ɗin take goyon baya a ƙasar Lebanon.

Hare-haren Isra’ila sun yi ajalin sama da mutum 200 a Lebanon, lamarin da ya sa jama’a gudun hijira zuwa ƙasar Syria, wadda a  baya mutanenta ke tsallakawa zuwa Lebanon sakamakon yaƙin basasa da ya ki ci ya ƙi cinyewa.

A makon nanne Iran ta yi ruwan makamai masu linzami a kan cibiyoyin soji da sauran wurare a Isra’ila, tana mai bayyana shirinta na shiga yaƙi idan Isra’ila ta kuskura ta kawo mata hari da sunan ramuwar gayya.

Ta bayyana cewa harin da ta kai wa Isra’ila gargaɗi ne cewa ta shiga taitayinta kan hare-hare da kashe-kashenta a Lebanon da yankin Zirin Gaza ba.

A yayin da Isra’ila ta lashi takobin ɗaukar fansa, Iran ta ce a shirye take su gwabza, duk da cewa ba ta son shiga yaƙi.

Iran ta kuma gargaɗi ƙasashen yankin Larabawa da cewa duk wadda a cikinsu Isra’ila ta yi amfani da sararin samaniyarta ko ta taimaka wa Isra’ila, to za ta yaba wa aya zaƙi.

Iran ta kai wa harin makamai masu linzami da suka girgiza matakan tsaron Isra’ila ne bayan Isra’ila ta kai munanan hare-hare a Lebanon da Yaman a cikin kwanakin nan.

A Yaman, Isra’ila ta kashe mutane sama da 90 tare da jikkata wasu 90, baya ta lalata manyan tashoshin wutar lantarki da cibiyoyin man fetur a yankin da ke ƙarƙashin ikon mayaƙan Houthi da ke da goyon bayan ƙasar Iran.

A Lebanon kuma ta hallaka sama da mutane 200 ciki har da shugaban ƙungiyar Hisbullah, Hassan Nasrallah, da wasu manyan jagororin kungiyar mai samun goyon bayan Iran.

Za kuma a iya tuna cewa Isra’ila ta kashe shugaban kungiyar Falasɗinawa ta Hamas, wadda Iran take goyon bayan, Ismail Haneiya, a birnin Tehran na ƙasar Iran, jim kaɗan bayan ya halarci taron kaddamar da sabon shugaban ƙasa.

Wannnan ɗori ne a kan kisan Falasɗinawa sama da 50,000 da sojojin Isra’ila suka kashe a yankin Zirin Gaza a cikin shekara guda daga ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Hare-haren Isra’ila sun rana Falsɗinawa sama da miliyan biyu da gidajensu a Zirin Gaza baya ga lalata kusan ɗauƙacin abubuwan more rayuwa kamar asibitoci da makarantu da wuraren ibada da wutar lantarki da ruwan sha da sansanonin gudun hijira da kasuwanni da sauransu.

A ranar 7 ga Oktoba 2023 ne mayaƙan Hamas suka kaddamar da wani mummunan harin ɗaukar fansa a Isra’ila, suka kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da wasu.

Hamas ta kaddamar da harin ne sakamakon kisan gilla da kwace matsugunan Falasɗinawa da tsare su ba bisa ka’ida ba da Isra’ila take yi tsawon shekaru.

Shin Binani ta dawo?

Sana’ar Bola-jari: Muna taka sawun barawo — Shugaban ‘yan gwangwan

’Yan sanda sun ƙwace sakamakon zaɓe a Ribas

Yadda mutanen Jigawa suka ƙi fita zaɓen ƙananan hukumomi