Iran da Turkiyya za su hada gwiwa don yakar ta’addanci

A wata ziyara mai cike da tarihi da shugaban kasar Iran ya kai kasar Turkiyya, kasashen biyu sun sha alwashin yin aiki tare don kawo karshen ayyukan ’yan ta’adda da kuma zubar da jinin da ake yi a yankin Gabas-ta-Tsakiya duk da banbamci ra’ayinsu kan yakin basasar kasar Siriya.Shugaban Iran Hassan Rouhani ya bayyana wa […]

Iran da Turkiyya za su hada gwiwa don yakar ta’addanci
Iran da Turkiyya za su hada gwiwa don yakar ta’addanci

A wata ziyara mai cike da tarihi da shugaban kasar Iran ya kai kasar Turkiyya, kasashen biyu sun sha alwashin yin aiki tare don kawo karshen ayyukan ’yan ta’adda da kuma zubar da jinin da ake yi a yankin Gabas-ta-Tsakiya duk da banbamci ra’ayinsu kan yakin basasar kasar Siriya.
Shugaban Iran Hassan Rouhani ya bayyana wa wani taron manema labarai a birnin Ankara inda ya ce “kasashen biyu suna da matukar mahimmanci a yankin saboda wannan ne muke ganin ya dace mu yi aiki tare don yakar ’yan ta’adda. Musamman ganin yadda ba wata kasa da take amfana tashe-tashen hankulan da ke faruwa a yankin.”  
Shugaban Turkiyya Abdullah Gul ya yaba wa kokarin Shugaba Rouhani  na  tallata Iran ga duniya tun bayan da ya zama shugaban kasa cikin watan Agustan bara.
Masu sharhi na ganin dangantakar kasashen biyu ta shiga halin ni-’yasu ne saboda ci gaba da fafutukar samun iko tsakanin ’yan Sunni da kuma ’yan Shi’a a Gabas-ta-Tsakiya. baraka ta barke tsakanin kasashen biyu ne bayan da kasar Siriya ta samu kanta cikin yakin basasa, inda kuma kasashen biyu suke goyon bayan bangarori mabanbanta.
kasar Iran, wadda take gwamnatin ’yan Shi’a ce, ita ce babbar mai mara wa Shugaba Basar al-Assad baya. A bangaren Turkiyya kuma wadda galibin ’yan kasarta ’yan Sunni ne tana goyon bayan mayakan ’yan tawaye ne masu dauke da makamai.
A mokon jiya, Mista Rouhani ya taya Shugaba Assad murnar lashe zabe, inda kuma kasashen Yamma suka bayyana zaben da wani wasan yara.