Iran ta ayyana hutun kwana uku domin jana’izar Ali Khamenei
Jana’izar da za a gudanar za ta zo daidai da Ranar ’Yancin Kan Amurka, wadda a bana ta cika shekara 250 da kafuwa.
Gwamnatin Iran ta sanar da ayyana hutun kwanaki uku a babban birnin ƙasar, Tehran, domin gudanar da bukukuwan jana’izar marigayi Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ali Khamenei.
Gidan talabijin ta gwamnatin Iran ya ruwaito cewa kwamandan rundunar juyin juya hali na ƙasar da ke jagorantar shirye-shiryen jana’izar, Hassan Hassanzadeh, ya ce za a gudanar da tarukan bankwana da addu’o’i ga gawar marigayin a ranar Asabar da Lahadi, 4 da 5 ga watan Yuli, a Babban Masallacin Musalla da ke Tehran.
Ya ce za a gudanar da jana’izar marigayin a ranar Litinin, 6 ga watan Yuli, yayin da za a dakatar da harkokin aiki a lardin Tehran na tsawon kwanakin uku domin bai wa jama’a damar halartar bukukuwan.
Tun da farko kafafen yaɗa labaran gwamnatin Iran sun bayyana cewa za a ayyana hutu a Tehran a ranakun 4 da 5 ga watan Yuli, yayin da hutun ranar 6 ga watan Yuli zai shafi ɗaukacin faɗin ƙasar.
Ana sa ran jana’izar Ali Khamenei za ta samu halartar dubban mutane daga sassa daban-daban na Iran da kuma baƙi daga ƙasashen waje.
A makon da ya gabata ne gwamnatin Iran ta sanar da cewa za a gudanar da jana’izar marigayi Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya jagoranci ƙasar tsawon kusan shekara 37 kafin rasuwarsa a harin sama da Isra’ila da Amurka suka kai a ranar 28 ga Fabrairu.
Rahotanni daga Iran sun ce tun farko an shirya gudanar da jana’izar ce a watan Maris, amma aka ɗage ta sakamakon yaƙin da ya dabaibaye ƙasar a lokacin.
A cewar rahotannin, za a gudanar da jana’izar ce ta tsawon kwanaki shida, daga ranar 4 zuwa 9 ga Yuli.
Za a fara da jana’izar ƙasa a babban birnin Tehran daga ranar 4 zuwa 6 ga Yuli, sannan a ci gaba da wasu bukukuwan girmamawa a birnin Qom, ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin addini na ƙasar.
Daga bisani, za a binne marigayin a ranar 9 ga Yuli a birnin Mashhad da ke arewa maso gabashin Iran, wanda shi ne garinsu na haihuwa.
Jana’izar ƙasar da za a gudanar a ranar 4 ga Yuli za ta zo daidai da Ranar ’Yancin Kan Amurka, wadda a bana ta cika shekara 250 da kafuwa.
Bayan rasuwar Ali Khamenei, ɗansa Mojtaba Khamenei ya gaje shi a matsayin Jagoran Ƙoli na Iran a farkon watan Maris, inda ya zama mutum na uku da ya riƙe muƙamin tun bayan kafuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shekarar 1979.
Rahotanni sun ce Mojtaba Khamenei ya samu raunuka a hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar mahaifinsa da wasu manyan jami’an ƙasar. Sai dai tun bayan naɗa shi, bai fito bainar jama’a ba, kuma ana fitar da saƙonninsa ne ta hanyar sanarwar da ake danganta masa.