Iran ta sa wa Amurka sabbin ka’idodin sulhu
Trump, ya bayyana a ranar Asabar cewa zai yi nazarin sabbin sharuɗɗan da Iran ta gabatar domin yanke shawarar da ta dace
Gwamnatin Iran ta sanya wa’adin wata guda domin cimma yarjejeniya da Amurka kan buɗe mashigin Hormuz da kuma kawo karshen toshewar da jiragen ruwan Amurka suka yi mata, da kuma dakatar da yaƙi a Iran da Lebanon.
Jaridar Axios ta ruwaito a ranar Asabar cewa Tehran ta miƙa wa Amurka sabbin ka’idodi 14 game da tsarin yarjejeniyar a ranar Alhamis.
Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana a ranar Asabar cewa zai yi nazarin sabbin sharuɗɗan da Iran ta gabatar domin yanke shawarar da ta dace.
“Idan Iran suka yi ba daidai ba, ko suka yi wani abu mara kyau…., amma yanzu dai za mu gani. Wata kila hakan zai iya faruwa,” in ji shi ga ’yan jarida da suka tambaye shi ko zai iya bayar da umarnin kai hare-hare.
- Ana binciken sojojin da ake zargi da hannu a hare-haren da aka kai Mali
- Kwankwaso: Ban yanke hukunci kan jam’iyyar da zan koma ba
Majiyoyi biyu da suka ga takardar sun bayyana cewa sharuɗɗan sun ƙunshi wa’adin wata guda kacal don tabbatar da yarjejeniya kan harkokin ruwa, kawo ƙarshen mamayar da jiragen ruwan Amurka suka yi, da kuma samun tsagaita wuta na dindindin a ɓangarorin biyu.
Shirin Iran ya kuma tanadi mataki na biyu bayan an kammala yarjejeniya ta farko, inda za a ƙara wata guda na tattaunawa kan shirin nukiliya, a cewar majiyoyin.
Sai dai a ranar Juma’a, Trump ya bayyana rashin gamsuwa da shirin Iran.
Amma a ranar Asabar kafin ya bar Palm Beach zuwa Miami, ya ce: “Ina duban sa. Zan sanar da ku daga baya. An fada min game da tsarin yarjejeniyar a dunƙule, amma nan gaba za su kawo min cikakken rubutun.”
Bayan haka, a shafinsa na Truth Social, Trump ya nuna tsaurin ra’ayi inda ya ce “ba zan iya tunanin cewa za a amince da shi ba,” tare da jaddada cewa Iran “ba ta biya laifin da ta aikata wa bil’adama da duniya cikin shekaru 47 da suka gabata ba.”
A cikin jawabin nasa ga manema labarai, Trump ya bayyana toshe tashoshin jiragen ruwan Iran a matsayin “mataki da ya samu karɓuwa” wanda ba a ƙalubalanta ba, yana mai cewa hakan bai saɓa wa ikirarin da yake yi cewa an “dakatar da faɗa” ba.