Iran ta ce ta dakatar da hare-hare bayan Amurka ta daina kai mata farmaki
Iran ta ce Amurka ta tsagaita da kai mata hare-hare cikin kwanaki biyu da suka wuce.
Iran ta ce ta dakatar da hare-haren da ta ke kaiwa, bayan Amurka ta daina kai mata hare-hare a cikin kwanaki biyun da suka gabata.
Kakakin rundunar sojin Iran ya ce hare-haren da ƙasar ta kai ramuwar gayya ne kawai, kuma yanzu sun tsaya.
- Sojoji sun ceto mutum 48 da aka sace a Zamfara
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da alƙalin babbar kotun Kebbi
Har yanzu gwamnatin Amurka ba ta bayyana a hukumance dalilin da ya sa ta dakatar da hare-haren ba, bayan kusan makonni biyu ana kai su.
Sai dai wasu kafafen yaɗa labarai na Amurka, sun ruwaito cewa Shugaba Donald Trump ne, ya ba da umarnin dakatar da hare-haren.
Rahotannin sun ce an nuna masa damuwa kan ƙarancin makaman kariya na Patriot da kuma yiwuwar ci gaba da hare-haren zai iya ɓata wa ƙawayen Amurka na ƙasashen Larabawa rai.
A wani ci gaba kuma, kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, ya ce ana samun ci gaba a tattaunawar da ake yi ta hannun ƙasar Oman kan yadda za a tabbatar da zirga-zirga cikin kwanciyar hankali a mashigar Hormuz.