Iran ta harba makamai masu linzami kan jiragen ruwa a Mashigar Hormuz

Lamarin na zuwa ne bayan tattaunawar Amurka da Iran a makon da ya gabata ta ƙare ba tare da cimma wata yarjejeniya.

Iran ta harba makamai masu linzami kan jiragen ruwa a Mashigar Hormuz

Rahotanni sun ce dakarun Rundunar Juyin Juya Halin Iran (IRGC) sun harba aƙalla makamai masu linzami biyu kan wasu jiragen ruwan kasuwanci da ke ratsawa ta Mashigar Hormuz cikin dare a Litinin.

Kafar yaɗa labarai ta Axios ta ambato wasu jami’an Amurka biyu da ke cewa harin ya lalata jiragen ruwa biyu, sai dai ba a samu asarar rayuka ba.

A safiyar Talata kuma, Hukumar Kula da Harkokin Kasuwancin Jiragen Ruwa ta Birtaniya (UKMTO) ta ce an kai hari kan wani jirgin ruwa da ya yi nisan tafiyar kilomita 15 gabas da yankin Limah na ƙasar Oman.

Hukumar ta ce harin ya haddasa gobara a jirgin, amma babu rahoton asarar rayuka ko gurɓata muhalli.

Lamarin na zuwa ne bayan tattaunawar da aka yi tsakanin Amurka da Iran a makon da ya gabata ta ƙare ba tare da cimma wata yarjejeniya ta dindindin ba, duk da tsagaita wutar kwanaki 60 da ake fatan za ta buɗe ƙofar sasanci bayan rikicin da ya biyo bayan hare-haren Amurka da Isra’ila.

A ranar Litinin, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ƙasarsa za ta cimma yarjejeniya da Iran ko kuma ta “kammala aikin”, yana mai sake jaddada matsayinsa yayin da Tehran ke ci gaba da nuna rashin amincewa.

Rahoton Jaridar The Wall Street ya ce dakarun IRGC sun yi gargaɗi ga jiragen ruwa ta hanyar tashar sadarwar ruwa a ƙarshen mako, inda suka ce:

“Mun shirya harba muku makamai masu linzami da jirage sama marasa matuƙa.”

Rahoton ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin jiragen ruwan da aka kai wa hari shi ne Al Rekayyat, wani jirgin dakon iskar gas mallakin Nakilat da ke jigilar iskar gas ta Qatar.

A cewar jaridar, “ɓangaren injin ya kama da wuta kuma ya cika da hayaƙi, abin da ya sa ba a iya tantance girman ɓarnar ba. Duk ma’aikatan jirgin suna cikin ƙoshin lafiya kuma an tattara su a wuri mai aminci a cikin jirgin.”

Rahoton ya ce jirgin yana kusa da Mashigar Hormuz, a Tekun Oman, lokacin da aka kai masa harin.

Masu zuba jari na ci gaba da sanya ido kan halin da ake ciki, musamman tattaunawar Amurka da Iran kan tsaron Mashigar Hormuz, yayin da ake bibiyar makomar fitar da ɗanyen mai daga ƙasashen yankin Gulf.