Iran ta karrama kwamandan da ya kai wa Isra’ila hari

A ranar Talatar da ta gabata ce rundunar ta harba wasu makamai masu linzami kimanin 200 kan Isra’ila a matsayin ramuwar gayya

Iran ta karrama kwamandan da ya kai wa Isra’ila hari

A handout picture provided by the office of Iran’s Supreme Leader Ayatollah Ali Khamenei on October 6, 2024 shows him (R)decorating the Islamic Revolutionary Guard Corps’ Aerospace Force Commander Brigadier General Amir Ali Hajizadeh (L) with the ‘Fath’ badge in Tehran for plannig the Iranian attack on Israel. – The Iranian general was decorated for the “brilliant operation” of “Honest Promise”, referring to two missile attacks carried out by Iran against Israel in April and October 2024. (Photo by KHAMENEI.IR / AFP) / === RESTRICTED TO EDITORIAL USE – MANDATORY CREDIT “AFP PHOTO / HO / KHAMENEI.IR” – NO MARKETING NO ADVERTISING CAMPAIGNS – DISTRIBUTED AS A SERVICE TO CLIENTS ===

Jagoran Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya karrama kwamandan dakarun kare juyin juya hali da ya jagoranci harin makami mai linzami da ƙasar ta kai wa Isra’ila.

Ayatullah Khamenei ya sanya wa Janar Amirali Hajizadeh aninin Fath (nasara), a ranar Lahadi.

An karrama Janar Amirali Hajizadeh ne saboda “kyakkyawan aiki na ‘Gaskiya'”, in ji shafin rundunar juyin juya halin Musulunci na Iran.

Hajizadeh, mai shekaru 62, ya shugabanci sashin kula da sararin samaniyar rundunar tun lokacin da aka ƙirƙiro shi a shekarar 2009.

A ranar Talatar da ta gabata ce rundunar ta harba wasu makamai masu linzami kimanin 200 kan Isra’ila a matsayin ramuwar gayya kan harin da Isra’ila ta kai ta sama da ta kashe shugaban kungiyar Hizbullah Hassan Nasrallah da kuma Janar Abbas Nilforoushan na rundunar a Beirut, babban birnin ƙasar Lebanon.

Wannan dai shi ne hari na biyu kai tsaye da Iran ta kai wa Isra’ila cikin watanni shida.

A watan Afrilu ta kai wani hari da makami mai linzami da jirgin sama mara matuki a matsayin ramuwar gayya kan wani mummunan harin da aka kai kan karamin ofishin jakadancinta da ke Damascus, babban birnin ƙasar Syria, wanda Tehran ta zargi Isra’ila.

Isra’ila ta sha alwashin mayar da martani bayan harin makami mai linzami da Iran ta kai ranar Talata.